Wani mara lafiya a Norfolk ya warke ya ki barin asibiti

James Paget
Bayanan hoto,

Asibitin koyarwa na jami'an James Paget da ke Ingila

Hukumomin wani asibiti a Norfolk da ke gabashin Ingila na yunkurin fitar da wani mara lafiyar da ya ki tafiya bayan ya warke.

Mutumin wanda hukumomin asibitin koyarwa na jami'ar james Paget da ke ingilar bai bayyana sunan shi ba, ya shafe shekaru biyu a gadon asibitin.

Hukumomin asibitin sun ce ya samu saukin da ya kamata a sallame shi kuma an bashi wurin kwanan da ya dace.

Sun ce yanke shawarar garzayawa kotu ita ce mafata ta karshe da suke da ita.

Tun a cikin watan Agustan shekara ta 2014 ne mutumin da ya fito daga yankin Gorlstone dake gundumar Suffolk ke kwance a asibitin.

Asalin hoton, Thinkstock

Bayanan hoto,

Yana asibitin tun cikin watan Agusta 2014 zuwa Janairu 2017

Wata mara lafiya dake daki daya da wannan mutum ta ce wannan '' sanannen abu ne'' cewa yana asibitin fiye da shekaru biyu.

Ta ce '' wannan abin mamaki ne da yake amfani da asibitin a matsayin otal".

Asibitin ta bukaci kotu ta bata ikon fitar da mutumin daga wurin kwanan da yake ke ciki.

Kotun ta ba da dama a ranar 1 ga watan Disamba, amma sun yi waje da shi a ranar 10 ga watan Janairu.