ECOWAS tana tattaunawar ƙarshe da Jammeh

Yahya Jammeh

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An rantsar da mutumin da ya kayar da Yahya Jammeh ranar Alhamis a ƙasar Senegal

Wasu shugabannin ƙasashen Afirka ta yamma sun je Gambia a ƙoƙarinsu na rarrashin Yahya Jammeh ya sauka daga mulki don bai wa magajinsa dama.

An bai wa Jammeh har zuwa yammacin Juma'a don ya tattara nasa-ya-nasa ya bar ofis ko dakarun Afirka ta yamma da Majalisar Ɗinkin Duniya ke mara wa baya su cire shi ta ƙarfin tuwo.

An tsawaita wa'adin ne ta yadda za a samu damar tattaunawar ƙarshe.

Dakarun sojan sun samu umarni a kan su dakatar da dannawar da suke yi cikin kasar har sai an kammala tattaunawa.

Kungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta yamma na mara baya ga sabon shugaban Gambia Adama Barrow, wanda aka rantsar a ranar Alhamis.

Ya samu halarci daga ƙasashen duniya a matsayin shugaban ƙasar da aka zaɓa a cikin watan jiya.

Shugaban ƙasar Guinea Alpha Conde da na Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz sun sauka a Banjul don ganawa da Yahya Jammeh.

Shugabar hukumar ECOWAS, Marcel Alain de Souza ya ce idan tattaunawar ta gaza samun nasara, sojoji za su ɗauki mataki.

Jawabin kama-aiki

A jawabinsa na farko don kama mulki Shugaba Adama Barrow ya ce: "Daga yau (Alhamis), Ni ne shugaban ƙasar Gambia ko ka/kin zaɓe ni ko ba ka/ki zaɓe ni ba."

Ya ce "Wannan nasara ce ga ƙasar Gambia.. mulki a hannun jama'a yake a Gambia"

A cewarsa "Wannan rana ce wadda babu wani ɗan Gambia da zai taɓa mantawa da ita... karon farko tun bayan samun 'yancin kai, Gambia ta sauya gwamnati ta hanyar ƙuri'a".

Shugaban ƙasa biyu

A ranar Laraba ne wa'adin Yahya Jammeh a kan mulki ya ƙare, ko da yake majalisar dokokin ƙasar ta tsawaita zamansa a kan mulki da kwana 90.

'Yan Gambia da ma 'yan kasashen waje da ke zuwa yawon bude ido a kasar da yawa ne suka fice zuwa wasu ƙasashe maƙwabta saboda tsoron ɓarkewar rikici.

Barrow ya kayar da Mista Jammeh a zaben da aka yi cikin watan Disamba.

Da farko dai Jammeh ya amince da shan kaye sannan ya taya Mista Barrow murna, amma daga bisani sai ya ce ba zai sauka daga mulki ba saboda zargin da ya yi cewa an tafka kura-kurai a zaben.

Ya kuma garzaya kotu inda yake kalubalantar sakamakon zaben.