Amurka zan sanya gaba da komai - Trump

Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Trump a lokacin da yake rantsuwa don kama aiki a matsayin shugaban Amurka

An rantsar da Donald Trump a matsayin shugaban Amurka na 45, inda ya yi alƙawarin sanya kasar a gaba da komai.

A wani jawabin ƙaddamarwa da ya saɓa wa ƙa'ida kuma cikin hasala, Mr Trump ya yi alƙawarin mayar da iko hannun jama'a daga Washington.

Ya kuma ci alwashin cewa a duk wani abu, ko duk wata shawara da zai ɗauka, zai tabbatar da sanya muradun jama'arsa a gaba da komai.

Sabon shugaban Amurka ya ce kare ƙasar zai janyo mata gagarumin bunƙasar arziƙi da ƙarfi, ya kuma lashi takobin dawo wa Amurka ayyukan yi da arziƙinta da tsare iyakokinta.

Cincirindon jama'ar da suka taru don shaida bikin rantsuwar a gaban ginin majalisun Amurka, Capitol Hill, sun riƙa yi masa sowa da tafi.

Bayanan hoto,

Wasu na nuna shakku kan ko Mista Trump zai iya aiwatar da manufofinsa

Wakilin BBC ya ce akwai alamar cewa Donald Trump zai yi mulki ne kamar yadda ay yi yaƙin neman zaɓe, ta hanyar cewa cas ga duk wanda zai ce masa kule!

Tsaffin shugabannin kasar da suka hada da Bush karami, da Jimmy Carter, da Bill Clinton duk sun halarci bikin rantsuwar.

Hakazalika Hillary Clinton, wacce ta sha kaye a hannun Mista Trump, ita ma ta halarta.

Sabon shugaban ne ya raka mutumin da ya gada Barack Obama wurin da ya shiga jirgi domin tafiya inda zai ci gaba da rayuwarsa.