Daliban kasar Italy 16 sun mutu a hadarin mota a arewacin kasar

Motar na kan hanyarta ta dawowa birnin Budapest daga kasar Faransa

Asalin hoton, VIGILI DEL FUOCO

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin daliban kuma sun makale a cikin motar ne a lokacin da ta kama da wuta

Wata motar safa dauke da dalibai ta yi hadari, ta kuma kama da wuta a arewacin kasar Italiya, tare da hallaka mutane 16, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Motar wacce ke dauke da daliban daga kasar Hungary, ta yi karo da wani ginshiki a lokacin da ta kauce daga kan titi a kusa da birnin Verona da yammacin ranar Jumma'a.

Hukumar kashe gobara ta kasar ta bayyana a shafinta na Twitter cewa mutane 39 kuma sun samu raunuka.

Motar safa din na kan hanyarta ta dawowa birnin Budapest daga kasar Faransa ne, inda daliban ke yin hutun yawon bude ido a kan tsaunuka.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Italiya Ansa, ya ce motar ta yi ta watsar da daliban da dama waje, da akasari maza ne masu shekaru daga kimanin 14 da 18, a lokacinda ta yi karo da ginshikin..

Har yanzu dai ba a gano dalilan da suka saka motar da kauce hanya ba.

Wasu daga cikin daliban kuma sun makale a cikin motar ne a lokacin da ta kama da wuta, inji kamfanin dillancin labari na Ansa.

Hukumar kashe gobara da kasar Italiyar ta ce babu alamun samun karuwar wadanda suka rasa rayukansu.

Kafar yada labaran kasar Hungary ta bayar da rahoton cewa yanzu haka jakadan kasar a birnin Milan ya isa birnin Verona.

Asalin hoton, VIGILI DEL FUOCO

Bayanan hoto,

Motar ta yi karo da wani ginshiki a lokacin da ta kauce daga kan titi a kusa da birnin Verona