Pakistan: Harin bam a wata kasuwa ya kashe mutum 20

Jiragen sojoji masu saukar angulu na ta kwashe wadanda suka samu raunuka, bayan harin bam din

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Kungiyar Taliban ta kasar Pakistan ta ce ita ke da alhakin kai harin a kasuwar danyen kaya ta Parachinar

Mutum 20 ne suka mutu yayin da wasu 40 suka jikkata, bayan fashewar wani bam a wata kasuwar danyen kaya a kasar Pakistan.

Lamarin ya faru ne a birnin Parachinar, yankin da ke kan iyakar kasar Afghanistan da akasari Musulmi 'yan Shia ne ke zaune .

Kasuwar makare take da masu sayayya a lokacin da bam din ya tarwatse.

Mahukunta sun ce adadin wadanda suka mutun ka iya karuwa.

Wani bangare na kungiyar Taliban a Pakistan ya yi ikirarin kaddamar da harin, tare da cewa wata manufa ce ta daukar fansa kan hallaka mutanensu.

Kakakin kungiyar ya yi kashedin cewa kungiyar za ta ci gaba da kai hare-hare kan 'yan Shi'a, muddin suna goyon bayan Shugaba Assad na Syria, wanda mulkinsa ya haddasa yakin basasa da kuma asarar rayuka fiye da 310,000.

Mene ne musabbabin fashewar bam din?

Rahotanni daban-daban da ke fitowa game da musabbabin fashewar bam din na danganta hakan ga wasu ababan fashewa da aka dasa a karkashin wani teburin sayar da danyen kaya.

Wasu bayanai kuma na cewa wani dan harin kunar bakin wake ne ya haddasa lamarin.

Sabir Hussain, wani likita ne a babban asibitin Parachinar, da ya shaida wa wani kamfanin dillancin labarai cewa mutum 11 da suka samu munanan raunuka sun mutu daga bisani a asibitin.

Ya kuma ce da dama da ke cikin mummunan yanayi an garzaya da su zuwa wasu asibitocin don kulawa da su sosai.

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Jami'an tsaron kasar Pakistan sun kewaye wurin da bam din ya tarwatse

Rundunar sojin Pakistan ta ce sojojinta sun kewaye wurin da bam din ya fashe, kuma jirage na kwashe wadanda suka samu raunuka.

A cikin watan Disambar shekara ta 2015 ne wani harin bam ya hallaka mutum 23, tare da jikkata fiye da 30 a wannan kasuwar.

Firai ministan Pakistan Nawaz Sharif ya fitar da wata sanarwa yana nuna jimaminsa kan asarar rayukna da aka tafka.