Wasan Swansea ya kada ni - Klopp

Liverpool da Swansea

Asalin hoton, Getty Images

Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce rashin nasarar da suka yi a gida a hannun Swansea da ci 2-3 ya kada shi kuma abin takaici ne.

Ya kara da cewa 'yan wasansa sun gajiya a yunkurinsu na kare gida, abin da ya sa suka kwashi kashinsu a hannu.

Gylfi Sigurdsson ne ya zura kwallo ta uku saura minti 16 a tashi daga wasan, abin da ya bai wa Swansea nasarar farko kan Liverpool a waje.

Tun da farko Roberto Firmino ya farke kwallaye biyun da Fernando Llorente ya zura cikin mintuna hudu bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

A yanzu Liverpool suna mataki na uku, maki bakwai tsakaninsu da Chelsea wacce ke mataki na daya, kuma sun yi wasa daya fiye da Chelsea.