Firaiminista kasar Mauritius zai mika mulki ga dansa

Pirai Ministan Mauritius Anerood Jugnauth a shekara ta 2015

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Mr Jugnauth ya kasance mai fada a ji a fagen siyasar Mauritius a cikin shekaru da dama

Firaiministan Mauritius Anerood Jugnauth ya ce zai yi murabus ya kuma mika ragamar mulkin ga dansa Pravind.

Mai shekaru 86, Mr Jugnauth ya fara zama firaiministan kasar a shekarar 1982.

A wani jawabi ta gidan talabijin, Mr Jugnauth ya ce zai yi murabus din ne saboda dansa '' matashi ne kuma gogagge a fannin shugabanci''

Yanzu haka kuma yana rike da mukamin ministan kudi ne a kasar.

Jam'iyun adawa sun soki wannan mataki, amma kuma ba za su iya yin komai a kai ba..

Tsohon firaiminista , Navin Ramgoolam, ya yi gargadin cewa iyalan na kokarin mayar da mulkin kasar Mauritius kamar wani gadon gidansu.

A ranar Litinin da safe ne ake sa ran Mr Jugnauth zai mika takardar yin murabus din nasa.