'Kafafen yada labarai sun fi kowa rashin gaskiya a duniya'

Hotunan taron bikin kaddamar da Trump da Obama da aka dauka daga saman hasumiyar Washington

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Taron kaddamar da Trump (hagu) da na Obama a shekara ta 2009 ( dama)

Shugaba Donald Trump ya zargi kafafen yada labarai game da nuna rashin gaskiya kan adadin mutanen da suka hakarci taron bikin rantsar da shi.

Mr Trump ya ce " da alamu mutane miliyan daya da rabi ne a wurin taron bikin rantsar da ni'', a lokacin da yake magana da wasu manyan jami'an gwamnatin Amurkar.

Daga bisani jami'in yada labaransa na fadar White House ya ce taron kaddamar da shugaba Trump din '' taro ne irin wanda ba a taba ganin irinsa ba a tarihi''.

Babu dai wanda ya bayar da wata shaida da za ta gaskata wannan ikirari, kana hotunan sun nuna yadda jama'a suka yi cincirindo lokacin bikin rantsar da Barack Obama a shekara ta 2009

'Kafafen yada labarai sun fi kowa rashin gaskiya a duniya'

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban Amurka Donald Trump ya kalubalanci kafafen yada labarai

Shugaba Trump ya kara nanata ra'ayinsa a kan 'yan jarida cewa '' suna cikin masu rashin gaskiya a duniya''.

Inda daga bisani kakakin fadar White House Sean Spicer ya kara kalubalantar kafafen yada labaran.

" Akwai maganganu da dama a kafafen yada labarai game da dora alhaki kan Donald Trump , ni kuma zan iya cewa taura biyu ba ta taunuwa. Za mu iya dora alhakin wasu abubuwa kan su kansu kafafen yada labaran.''

Miliyoyin jama'a ne a Amurka da fadin duniya suka shiga zanga-zanga don nuni da bukatar 'yancin mata, da wasu masu fafutika ke amanna cewa na cikin barazana a sabuwar gwamnatin kasar.

Gangami mafi girma a Amurka an gudanar da shi ne a birnin Washington DC, da mahukuntan birnin suka kididdige cewa mutane sun kai kimanin 500,000, sai kuma birnin New York da ke biye da shi da 400,000, kana daruruwa a wasu wuraren da suka hada da biranen Chicago da Los Angeles.