Niger: Ana zargin wasu jami'ai 40 da almundahana

Gwamnatin jamhuriyar Niger din ta gudanar da bincike kan wasu ma'aikatunta
Bayanan hoto,

Hukumomin a Niger na zargin jami'an gwamnati 40 da almundahana da kudade

Hukumar 'yan sanda a jamhuriyar Niger PJ , na gudanar da bincike kan wasu jami'ai bisa zargin aikata almundahana da wasu makudan kudade.

Mutanen su kimanin 40 ne da suka hada da manyan jami'an gwamnati, da manyan 'yan kasuwa, da tsofaffin ministoci, da tsofaffin 'yan majalisar dokoki.

Wata majiyar hukokomin shari'ar kasar ta tabbatarwa da BBC cewa, wani bincike ne da gwamnatin ta aiwatar a wasu ma'aikatunta ya zargi mutanen da aikata ba daidai ba wajen sarrafa kudade da dukiyoyinta a cikin ma'aikatun.

Daga ciki akwai ma'aikatar tanadi da tsimin cimaka , inda gwamnati ta binciki yadda shugabannin suka sarrafa wasu dukiyoyin gwamnatin daga shekara ta 2007 zuwa 2011, da kuma daga shekara ta 2011 zuwa 2015.

Daya ma'aikatar da binciken ya shafa ita ce CAIMA, da ke samar da takin zaman, da iri, da sauran kayyakin ayyukan noma, inda aka gano tabargaza iri-iri.

Har ila yau a hukumar kula da ayyukan ginin madatsar ruwa ta Kandaji, binciken ya gano salwantar wasu makudan kudade da gwamnatin ta ware , domin bai wa talakawan da ayyukan ginin masatsar ruwan ya shafa diyya.