Hikayata 2016: Labarin Ranar Juma'a

Hikayata 2016: Labarin Ranar Juma'a

A ci gaba da karanto muku gajerun labaran da suka yi rawar-gani a gasar BBC Hausa ta farko ta rubutun kagaggen labari ta mata zalla, a yau muna kawo muku karatun labari na gaba a cikin 12n da alkalian gasar suka ce sun cancanci yabo.

Labarin na yau shi ne "Ranar Juma'a" na Patima Adamu, Unguwar Gini, birnin Kano, Najeriya, Badariyya Tijjani Kalarawi kuma ta karanta.