Yadda mazauna Lagos ke fama da matsalar karancin muhalli?

Lagos city
Bayanan hoto,

Ana gina Eko Atlantic da ke tsibirin Victoria domin cike gibin da ake da shi na muhallai

Lagos ne birni mafi girma a Najeriya, sai dai kuma ana fama da matsalar karancin muhalli. Wakiliyar BBC Nancy Kacungira ta duba yadda 'yan kasuwa ke kokarin shawo kan matsalar.

Samun gidajen haya da ba a biyan kudi da yawa wani kalubale ne a biranen da ke da yawan mutane, kuma an fi samun hakan a jihar Legas da ke Najeriya.

Sama da mutane 500,000 na komawa birnin a duk shekara, kuma an kiyasta cewa mutane miliyan 17 ne suke fama da matsalar karancin muhalli.

A na ci gaba da gine-gine domin shawo kan matsalar; daya daga cikin matakan da aka dauka shine na kirkirar fili daga teku domin gina wani sabon birni da aka yi wa lakabi da Eko Atlantic a tsibirin Victoria.

An cike wani bangaren tekun da ake so a kirkiri birnin ne da yashi da duwatsu domin a samu filin da girmansa ya kai sikwaya mita da nisan kilomita 10 wanda za a gina shaguna da gidaje da ofisoshi a kai.

Eko Atlantic wanda aka gina katanga tsakaninsa da teku mai tsayin kilomita 8 zai samar da wutar lantarki da ruwa da kuma hanyoyi masu zaman kansu.

Bayanan hoto,

Eko Atlantic zai iya bai wa mutane 500,000 muhalli

Eko Atlantic zai iya daukar nauyin muhallan da sama da mutane 500,000 za su zauna, amma ginin wanda zai lashe biliyoyin daloli, ana masa kallon unguwar "masu hannu da shuni".

Ronald Chagoury Jr, daya daga cikin masu aikin ginin ne kuma ya ce suna ta kokarin su ga cewar sun sauya tunanin mutane na cewar unguwar masu kudi ce.

"Tun da fari mun yi tunanin cewa birnin zai kasance na masu matsakaicin samu ne.''

"Mun san cewa masu matsakaicin samu suna ci gaba da bunkasa sosai a shekaru 15 da suka wuce kuma mun san cewa zasu fi haka bunkasa ma".

Rayuwa tare kakanni

Bayanan hoto,

Akwai gidaje da dama a Legas sai da akasarinsu babu kowa a ciki saboda mutane ba su da kudin biyan haya

Har yanzu wasu mazauna Lages na ganin cewa akwai isassun muhallai da mutane za su iya zaba amma basu da kudin da zasu iya biya ne.

Gidaje suna da tsada kuma akasarin masu gidajen haya na so a biya kudin hayar shekara biyu ne ba wai na wata ba.

Abimbola Agbalu, wani mai bayar da shawarwari ne a kan harkokin banki, kuma ya shaida min cewa tilas yake zaune tare da kakarsa saboda hayar gidan kansa zai yi tsada sosai.

"Idan har ina so na yi hayar gida a unguwar da nake so na zauna a Legas zan rika kashe kashi 80 cikin 100 na albashina saboda dole sai dai na biya kudin shekara biyu da dai sauransu.

"Daga nan kuma dole sai na kashe kashi 60 zuwa 70 cikin albashina a duk shekara domin na biya kudin hayan gida, kuma hakan bai yi ma'ana ba.

"Matsalar ba wai babu gidaje bane. Idan kika duba, zaki ga cewa akwai gidaje da dama da babu mutane a ciki a Legas, wasu ma su kan kai sama da shekara ba tare da an bayar da hayarsu ba.

"Matsalar ita ce mutane basu da kudin da za su biya ne. Muna bukatar mafita".

Gidajen kwantena

Bayanan hoto,

Ana tsawalla kudi a gidaje da dama da ake ginawa a Legas

Wani kamfani a Najeriya na kokarin neman mafita na gidaje masu saukin kudi ta hanyar gyara kwantenoni su zama kamar gidaje.

Dele Ijaiya-Oladipo ya ce shi ya samar da kamfanin Tempohousing da ke Najeriya domin magancewa masu matsakicin samu matsalar tsadar muhalli.

"Hanya daya da za a bi domin cike gibin da ake da shi wajen karancin muhallai ita ce wajen samar da gidaje masu inganci da saukin kudi.

"Bai dace a gina miliyoyin gidaje kuma a saka musu kudin hayar da babu wanda zai iya biya ba- ba za a cimma wata manufa ba idan har aka yi hakan,'' in ji Mista Dele.

Gidan kwantenonin da Mr Ijaiyi- Oladipo ke ginawa sun fi saukin kudi da kashi 25 cikin 100 a kan gidanjen da ake ginawa kuma ana iya gina su a cikin makwanni biyu.

"Sai dai har yanzu gidajen kwantenoni wani sabon abu ne ga 'yan Najeriya saboda haka mutane da dama na hayar kwantenonin su yi amfani da su a matsayin ofis.

"Muna bai wa mutane kwarin gwiwa domin su ziyarci ofis dinmu wanda aka yi da kwantena, ta yadda za su gane abin da muke nufi".

Legas ne birni mafi girma a Afirka kuma ana sa ran yawan mutanen garin zai karu zuwa shekarar 2050, hakan kuma zai kara matsi na zabin da mutane ke da shi na muhalli.