Ko Kenya za ta ci gaba da bai wa Kakar Obama kariya?

Mrs Sarah Obama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Kakar tsohon shugaban Amurka Barack Obama za ta ci gaba da samun kariya a kasar Kenya

Kakar tsohon shugaban Amurka Barack Obama za ta ci gaba da samun kariya, kamar yadda jaridar Standard ta kasar Kenya ta ce ta ji daga wasu majiyoyin gwamnati.

An kewaye gidan Sarah Obama a kauyen Kogelo, a gundumar Siaya da ke yammacin kasar, inda daga bisani ta rika samun kariyar sa'o'i 24 daga 'yan sanda, bayan da jikanta ya zama shugaban Amurka na 44.

Za a ci gaba da tantance masu ziyarar gidan nata a caji ofis din da ke wajen gidan, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Shugaban rundunar 'yan sandan yankin Joseph Sawe ya shaida wa jaridar cewa za su rika ziyartar Mrs Obama su rika ganin halin da take ciki.

"Za mu ziyarci Mama Sarah cikin mako mai zuwa, don mu ga halin da take ciki, bayan sauka daga mulki da jikanta ya yi,'' a cewar Mista Sawe.

Kauyen Kogelo na ci gaba da jan hankulan masu yawon bude ido, da ke son ganin ko daga ina mahaifin Mista Obama, wanda yake magana a kai a cikin littafinsa 'Dreams From My Father' ya fito.