An gano yadda durwar teku ke barbara da tsuntsun Penguins

Tsuntsun penguin

Asalin hoton, Thebeccamurray / CC by 2.0)

Bayanan hoto,

Masana kimiyya za su iya kintace ne kawai game da dalilin da ya sa Durwan tekun ke barbarar tsuntsayen na Penguin

A yanki mai tsananin sanyi a bangaren Antatika, a wani kebabben wuri, musamman tsibirin da aka kaurace masa, an gano yadda zakuwar Durwar teku 'seals' ta kai makura wajen barbara.

Kai tsaye, suna ta kokarin barbara da tsuntsayen penguins.

An samu fiye da durwar teku 'seal' guda da aka samu yana yin wannan aiki, a lokuta da dama.

An kuma samu daukar hoto, inda aka tattara cikakkun bayanan da aka wallafa a mujallar halittun yanki mai tsananin sanyi ta Polar Biology.

Ta yiwu yin hakan zai rage musu takaicin zakuwar barbara.

Dabi'ar son barbara da durwar seals ke da ita ba ta bai wa masana ilimin kimiyyar da suka tattara bayanai akai mamaki ba.

A shekarar 2006, sun gani, a karo na farko yadda durwar seal ya yi ta yunkurin barbara da babban tsuntsun penguin a tsibirin Marion, wani yanki na tsibirin Antatika inda ake samun wadannan daukacin halittun.

Asalin hoton, Liam Quinn / CC by 2.0)

Bayanan hoto,

Dabi'ar barbara da durwan tekun ke da ita ba ta bai wa masana kimiyyar da suka tattara bayanai akai mamaki ba

Sai dai sababbin hujjoji da aka wallafa game da binciken: "Yawan aukuwar tursasawar jima'i da babban tsuntsun penguin ke samu daga durwar seals," har yanzu yana bai wa masu bincike mamaki.

"A gaskiya ban a sa ran ci gaba da bibiyar irin wannan lamari da ya auku a shekarar 2006 ba, domin za a ci gaba da maimaitawa, duk da yake ba za a yi da yawa ba," a cewar Nico de Bruynm, daga cibiyar nazarin dabbobi masu shayarwa a Jami'ar Pretoria da ke Afirka ta Kudu.

A bagire uku, gungun masu bincike karkashin jagorancin William A. Haddad de Bruyn sun hango matashin durwar seals na yi wa lafiyayyen tsuntsun penguin wanda ba a tantance jinsinsa ba (mace ko namiji) tursasawar barbara.

Al'amura biyu sun auku a gabar ruwa ta ''Goodhope'' da kuma daya gefen teku na Funk, al'amarin da ya auku a shekarar 2006 ya faru ne a gefen teku daban-daban da aka maimaita, a wurin da ake kira Trypor.

"Wannan ya sanya mun kara jan damara don lura," inji de Bruyn da yake bayani game da wani sabon al'amari da ya sake aukuwa.

Daukacin al'amura uku da suka faru game da irin wannan yanayin, kowane lokaci a kan samu durwar seal na kai farmaki, ya kama ya dare tsuntsun penguin, dagan nan sai durwar seal ya yi yunkurin barbara a lokuta da dama, al'amarin da ake karkarewa a kimanin mintuna biyar, tare da yin hutu a tsakani.

''Ina da tabbacin cewa wannan dabi'a na yawan karuwa''.

Mace da namijin tsuntsun penguin suna yin barbara ne ta wata al'aura da ake kira cloaca, kuma akwai hasashe mai karfi cewa, wannan shi ne gaskiyar lamari kan yadda tsuntsun penguin ke yin barbarar, wadanda Haddad ya dauki fim dinsu.

A yanayi uku daga cikin hudu da aka tattara bayanai game da lamarin karshe durwar seal ya kyale tsuntsun penguin, amma a daya daga cikin al'amuran da suka auku, durwar seal ya cinye tsuntsun penguin bayan da ya yi yunkurin yin barbarar.

Durwan seal ya sha kama tsuntsun penguin ya cinye shi a wannan tsibiri.

Asalin hoton, Liam Quinn/CC by 2.0

Bayanan hoto,

Masana kimiyya za kawai su iya yin kintace ne kan dalilin da ya sanya durwan seals suka kwatanta wannan dabi'a.

Wadannan al'amura suna nuni da lokacin da aka samu gungun durwar seal da zakin teku (sea-lion) sun yi barbarar dabbar da ba ta cikin rukunin halittu irin su, kamar a wannan yanayi da dabba mai shayarwa ta yi yunkurin barbara da tsuntsu.

Masana kimiyya za kawai su iya yin kintace ne kan dalilin da ya sanya durwar seals suka kwatanta wannan dabi'a.

Sai dai sabon binciken da aka gudanar ya yi nuni da cewa yin barbara da tsuntsun penguin kokarin koyo ne (barbara) a tsakanin durwar seals da ke tsibirin.

"Durwan seals na da karsashin koyo - mun fahimci wannan daga dabi'ar dabbbobi ta neman abinci a misali," kamar yadda de Bruyn ya yi bayani.

Wannan ta yiwu shi ne dalilin da ya sanya aka samu aukuwar lamarin da yawa. "Ina da tabbacin jin cewa lamarin na kara aukuwa."

Amma " Idan wannan dabi'a ce ta koyo, a gaskiya ba za mu samar da fahimta tabbatatta kan da fa'idar wadannan matasa ke samu ba," inji shi. A cewarsa: "Fiye da ta yiwu a ce suna da fahimtar cewa wadannan tsuntsaye za su ba su damar aiwatar da dabarunsu na barbara."

Durwar seal ba su girma (nisan shekaru ko tsufan) ko yawansu ya kai yadda za su killace dimbin matan durwar seals, kamar yadda de Bruyn ya bayyana.

"Ta yiwu dabi'ar huce takaicin zakuwar barbara ce, bisa la'akari da sinadaran zumudi da ke bijiro musu a yanayin hayayyafarsu. Abu ne mawuyaci su kasa gane abokin barbara, wato daukar cewa tsuntsun penguin shi ne ta macen durwar seal.

"gaba daya zai yi wuya a ce ga hakikanin gaskiyar lamarin," in ji shi.

Asalin hoton, Liam Quinn / CC by 2.0)

Bayanan hoto,

Ta yiwu dabi'ar huce takaicin zakuwar barbara ce, bisa la'akari da sinadaran zumudi da ke bijiro musu a yanayin hayayyafarsu

Daukacin hotunan bidiyon ana danganta asalinsu daga William A. Haddad, a Mujallar Halittun yanki mai tsananuin sanyi ta Polar Biology.

Matta Walker Edita ne kan al'amuran doron kasa na BBC.