An bindige jarumin fim a yayin daukar wani bidiyo

'Yan sanda a titin Eagle Lane, a nirnin Brisbane

Asalin hoton, 9news.com.au

Bayanan hoto,

'Yan sanda a titin Eagle Lane, a nirnin Brisbane na kasar Australia

Wani jarumin fim ya mutu bayan harbinsa a kirji da aka yi, yayin daukar wani fim din waka a tsakiyar birnin Brisbane na kasar Australiya.

Mutumin mai kimanin shekaru ashirin da kadan, ya samu munanan raunuka a kirjinsa, bayan da aka harbe shi a wani wurin shakatawa na Brooklyn Standard da ke layin Eagle Lane a tsakiyar birnin.

Bidiyon na wata kungiyar mawakan hip hop ne Bliss n Eso da ke zaune a birnin Sydney.

Kungiyar mawakan ta fitar da wata sanarwa ga kafafaen yada labaran Australiya tana tabbatar da mutuwarsa.

"Yanzu haka tawagar masu shirya daukar bidiyon na aiki tare da 'yan sanda a binciken da suke gudanarwa, amma ba za su iya bayar da karin wasu bayanai ba, in ji sanarwar.

Ta ce mambobin tawagar ba sa wurin lokacin da abin ya faru.

Sifeton 'yan sanda Armitt ya shaida wa manema labarai cewa suna kan gudanar da bincike kan aikata miyagun laifuka.

"Ba mu san takamaimen yadda hakan ta faru ba a halin yanzu, amma muna kan binciike,'' ya ce.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mawakan Bliss N Eso sun samu lambobin yabo na Aria da dama

Ya ce 'yan tawagar masu shirya daukar bidiyon sun yi kokarin farfado da shi, amma sakamkon raunukan da ya samu daga bisani rai ya yi halinsa.

Sifeto Armitt ya ce har yanzu ba a gano ko sau nawa aka harbi mutumin ba.

Babu dai wanda ya samu ko da kwarzane a cikin 'yan tawagar, kuma babu wanda ya fuskanci barazana a cikin 'yan kallon, in ji 'yan sanda.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Australiya Associated Press, ya ambato ganau na cewa ya ji wata babban kara.

Mai aikin gine-gine Blake Shaw na aiki a saman ginin gidan shakatawar a lokacin da lamarin ya faru.

"Na ji karar harbi kamar sau uku, daga nan bayan minti biyar 'yan sanda suka iso'', ya ce.

Ya ce lokacin da ya leka ta wata kafa, ya hangi kudade a warwatse a kasa, yayin da jini ke malala a jikin mutumin.