Gambia: Shugaba Adama Barrow ya koma gida

Adama Barrow ya isa Banjul.

Asalin hoton, Adama Barrow

Bayanan hoto,

Adama Barrow ya ce a yanzu ya hadu da 'yan uwansa al'ummar Gambia

Shugaban Gambia Adama Barrow ya koma gida - kwanaki bayan da ya mutumin da ya gada Yahya Jammeh ya bar kasar domin fara gudun hijira a Equatorial Guinea.

Jirgin da ke dauke da shugaban ya isa Banjul, babban birnin kasar, inda dinbin jama'a suka yi dafifi domin tarbarsa.

Bayan ya sauka, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: "A karshe na isa gida #Gambia."

Misa Barrow, wanda ke zaune a makwabciyar kasar Senegal, shi ne ya lashe zaben watan Disamban da ya gabata.

Sai dai an smau tsaiko wurin rantsar da shi bayan da Mista Jammeh, wanda ya shafe shekara 22 a kan mulki, ya ki sauka.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban Senegal Macky Sall, daga dama, ya yi ban-kwana ga Mista Barrow a filin saukar jiragen sama na Dakar

Ya tafi gudun hijira a karshen mako bayan da shugabannin kasashen yammacin Afirka suka shawo kansa ya hakura.

Wasu rahotanni sun ce Mista Barrow zai fara zama ne a gidansa, yayin da ake tantance gidan shugaban kasa don gudun duk wani hadari ko matsala bayan ficewar Mista Jammeh.

A bangare guda dubban sojojin kungiyar ECOWAS na cigaba da zama a kasar dan tabbatar da tsaro.

Rahotani sun ce akwai tarin 'yan gani-kashenin tsohon shugaban a cikin jami'an tsaron kasar.

Jakadan majalisar dinkin duniya a yammacin Afirka Muhammad Ibn Chambas, wanda ya ce majalisar za ta taimaka wajen tabbatar da tsaro a Gambiar, shi ne ya raka Shugaba Barrow.