An tuhumi wani mai goyon bayan Trump da cin zarafin wata Musulma

Filin jiragen sama na JFK a Amurka

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Zai iya fuskantar daurin shekaru hudu idan aka same shi da laifi

An gurfanar da wani mutum dan jihar Massachusetts ta Amurka bisa zargin tsare wa da kuma haurin wata Musulma da kafa a filin saukar jiragen sama na JFK da ke New York.

An kuma zargi Robin Rhodes, mai shekara 57, da cewa "Trump... zai fatattake ku gaba daya," sannan ya hana matar fita daga ofishinta da ke sashin hutawar matafiya na Delta Sky Lounge.

Yana fuskantar tuhumar cin zarafi da kuma kulle mutum da bisa ka'ida ba, a cewar mai shari'a na Gundumar Queens.

Zai iya fuskantar daurin shekara hudu idan aka same shi da laifi.

Ita dai ma'aikaciyar ta Delta Airlines na sanye da dan kwali ne ko hijabi a ofishinta a ranar Laraba da daddare lokacin da lamarin ya faru.

An zargi Mista Rhodes da zuwa kofar ofishin, inda ya daki kofar, sannan ya tare hanya ya hana ta fita, kafin daga bisani ya dake ta da kafa sannan ya gaya mata bakaken maganganu.

Bayan da wani mutum ya shiga tsakani, sannan ta tafi, sai ya bita inda ya zauna a kan gwiwowinsa, yana kwaikwayon zaman sallah da Musulmi ke yi.

Tun bayan nasarar da Mista Trump ya samu a watan Nuwamba batun cin zarafin baki da Musulmi ya karu a kasar.