Manyan ministocin Trump na son ci gaba za zaman Amurka a NATO

Donald Trump

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

To ko wannan zai sa Trump sauya matsayi kan kawancen na Nato?

Tsohon Janar din sojin da Donald Trump ya bayar da sunansa a zaman wanda zai nada ministan tsaro James Mattis, ya buga wa sakataren tsaron Burtaniya Sir Micheal Fallon waya domin tabbatar da masa da cewa Amurka na nan daram a kungiyar NATO.

Sun yi tattaunawar ne kwanakki ukku kafin Theresa May ta zama shugabar kasar waje ta farko da za ta gana da Donald Trump domin tattaunawa da shi a fadar White House wadda ake fatan Ita ma ta kara jaddada muhimmancin kawancen a lokacin ganawar tasu ranar Jumu'a mai zuwa.

James Mattis dai ba shi ne kadai mukarrabin Donald Trump da ya nuna goyon bayan kawancen wanda shugaban da kasarsa ya kira maras rana kuma wanda lokacinsa ya wuce ba.

Shi ma Rex Tillerson- shugaban wani katafaren kamfanin danyen mai da ke Texas- wanda Trump zai nada a zaman sakataren harkokin waje mai goyon bayan kungiyar Nato ne.

Rantsar da Shugaban CIA

Kasancewar Mr. Tillerson ya samu kwamitin harkokin wajen majalisar dokoki ya amince da nadinsa a zaman sakataren harkokin waje duk da yake da dan kankanin rinjaye, ana sa ran majalisa ta tabbatar da nadinsa a makon gobe duk da damuwar ake nunawa kan alakar kasuwancin da ke tsakaninsa shugaban Rasha Vladimir Putin.

An rantsar da wanda Trump ya zabo domin shugabantar hukumar leken asiri ta CIA, wani dan majalisar wakilai Mike Pempeo daga jihar Kansas a daren Litinin bayan da majalisar ta tabbatar da nadinsa.

An dai samu tsaiko wajen tabbatar da nadin nasa saboda damuwar da aka nuna kan goyon bayan amfani da nutsar da wadanda ake tuhuma a ruwa domin tatsar da bayanai da dai sauran dabarun azabtarwa da yake yi.