Tsohon shugaban Amurka George HW Bush ya soma samun sauƙi

Asalin hoton, Reuters
George HW Bush da Barbara Bush sun yi aure shekara 72 da suka wuce
Likitoci a wani asibitin Texas sun ce tsohon shugaban kasar Amurka George HW Bush ya samu saukin da za a iya fitar da shi daga dakin kula da marasa lafiya na gaggawa.
Sun ce za a iya sallamar tsohon shugaban, mai shekara 92, wanda aka kwantar a asibiti sakamakon kamuwa da cutar sanyin hakarkari ranar 14 ga watan Janairu nan ba da dadewa ba.
An sanya wa shugaban Amurkar na 41 wata roba da ke taimaka masa yin numfashi.
Tuni dai aka sallami matarsa, Barbara Bush, mai shekara 91, wadda aka kwantar da su a asibiti tare.
Likitoci a asibitin na Houston Methodist sun gaya mata cewa za ta iya tafiya gida ranar Lahadi, amma ta kara kwana daya a asibitin domin ta kara murmurewa kana ta zauna kusa da mijinta.
Mr Bush, wanda ya zama shugaban Amurka tsakanin 1989-93, ya shafe mako daya a wani asibiti a jihar Maine a shekarar 2015 bayan ya karya kashin wuyansa sakamakon faduwar da ya yi.
Haka kuma yana fama da cutar mantuwa wato Parkinson's sannan yana amfani da keken guragu.