Kotun Koli ta kawo cikas kan fitar Birtaniya daga Turai

Alkalan kotun kolin Birtaniya

Asalin hoton, Supreme Court

Bayanan hoto,

Kotun Kolin ta ce dole majalisa ta tofa albarkacin bakinta

Kotun Kolin Birtaniya ta ce dole ne majalisar dokokin kasar ta yi muhawara kan matakin kasar na ficewa daga Tarayyar Turai.

Wannan hukuncin na nufin Firai Minista Theresa May ba za ta iya tattaunawa da Tarayyar Turai kan batun, sai 'yan majalisar dokokin sun goyi bayan ficewa daga kungiyar - koda yake ana sa ran za su amince da matakin kafin wa'adin da aka dibar wa kasar ta fita daga Tarayyar, wato ranar 31 ga watan Maris.

Da yakke yanke hukuncin, shugaban Kotun Kolin Lord Neuberger ya ce: "Alkalai takwas cikin 11 sun sun yanke hukunci a yau cewa Gwamnati ba za ta iya fita daga Tarayyar Turai ba sai tare da amincewar majalisar dokoki."

Amma kotun kolin ta ce ba sai majalisar dokokin Scotland da ta Wales sun kada kuri'a kan batun ba.

Masu fafutika sun ce hana majalisar dokokin Birtaniya kada kuri'a kan batun ya sabawa mulkin dimokradiyya.

Sai dai gwamnati ta ce tana da ikon daukar matakin ficewa daga Tarayyar ta Turai ba tare da samun goyon bayan majalisar dokokin ba.

Antoni Janar Jeremy Wright ya ce gwamnati ba ta ji "dadin" hukuncin ba, amma za ta yi biyayya a gare shi.