Morocco ta fitar da Ivory Coast daga AFCON

'Yan wasan Morocco na cike da kuzari

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan wasan Morocco na cike da kuzari

Morocco ta doke Ivory Coast da ci 1-0 inda ta kai matakin dab da na kusa da karshe a gasar cin kofin Afirka.

Rachid Alioui ne ya zura kwallon daga nisan yadi 25 abin da ya bai wa Morocco nasara.

Tun kafin wasan, Ivory Coast na bukatar ta ci kwallo daya idan tana son matsawa zuwa mataki na gaba, amma hakan bai samu ba.

Wilfried Zaha ya doka kwallo daga yadi 12, yayin da shi ma Salomon Kalou ya buga wata kwallo da kansa koda yake ta kaucewa raga.

'Yan kungiyar kwallon kafar ta The Elephants ba su yi wasa da kuzari ba.

Morocco ta yi wasan ne cike da masaniyar cewa idan suka yi kunnen-doki za ta iya kai matakin kwata-fainal don haka 'yan wasanta sun yi wasa mai armashi.

Yanzu dai za su fafata da duk kungiyar da ta yi nasara a rukunin D ranar Lahadi.

Ita ma DR Congo ta zo ta daya a rukunin C, bayan ta doke Togo 3-1.