Afirka ta Kudu ta hana China fataucin naman Jaki

Afirka ta Kudu

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An gano fatar jaki sama da 5,000 a cikin wani wurin ajiya a wata gona da ke kusa da birnin Benoni a lardin Gauteng.

'Yan sanda a kasar Afirka ta kudu sun gano wasu 'yan China masu fatauci da kasuwancin fata da naman jaki.

An gano fatar jaki sama da 5,000 a cikin wani wurin ajiya a wata gona da ke kusa da birnin Benoni a lardin Gauteng.

Babu wanda aka kama amma masu binciken suna fatan cewa ma'aikatan gonar za su iya gane wadanda ke aike wa da fatun a cewar jaridun Mail da Guardian.

An tara kuma aka boye fatun, wanda aka wanke tsaf da gishiri a bayan wasu tsoffin kujeru da wasu kayan aikin gona.

China tana amfani da sinadarin gelatin da ake samu a jikin jaki wajen hada magunguna da magungunan kara ni'imar mata da kuma mayukan hana alamun tsufa.

Kasuwancin wanda ake yi a halasce kuma wasu lokutan a haramce na da darajar miliyoyin daloli, sai dai yana barazana ga yawan jakai da ke wasu kasashen Afirka.

A bara ne dai Najeriya da Burkina Faso suka hana fitar da jakai daga kasashen.

China ta dade a kasuwanci

Bayanan hoto,

A bara ne dai Najeriya da Burkina Faso suka hana fitar da jakai daga kasashen.

Ba wannan ne karon farko da bukatar da China ke yiwa jakuna ke jawo ce-ce-ku-ce a baya-baya nan ba.

A watan Satumbar da ya gabata ne dai Nijar ta hana fitar da jakai, inda ta yi gargadi cewa ninki da aka samu a kasuwancin yana barazana a yawan jakunan da take da su.

Sinadarin gelatin da ake samu daga jikin jaki na matukar tsada a China a matsayin wani sinadarin magani wanda ke inganta jini da kara karfin garkuwar jiki da kuma kara kuzari.

A wasu lokutan ana kiransa "Three nourishing treasure".

Ana samar da sinadarin gelatin da ya yi fice ne a yankin Dong'e da ke Arewa maso Kudancin lardin Shandong, inda ake yin sa da ruwan rijiyar garin.

Ana hada Sinadarin gelatin da wasu 'yan'yan itatuwa da abinci mai kara jini a sayar da shi a matsayin abin kwadayi.

'Cimaka da naman jaki'

Lafiya da tsawon rai abubuwa ne da 'yan China dauka da muhimmanci, kuma wasu lokutan a kan hada kayan kwalam da makulashe masu tsada sosai da sinadarin domin 'yan kasar kan bayar da shi a matsayin kyauta.

Baya ga gelatin, wasu lardunan China na cin naman jaki, musamman a arewacin kasar.

A wadannan lardunan, a kan jika naman a ruwan nama mai dauke da kayan kamshi, idan ya huce sai a yayyanka a rika dangwala a hadin tafarnuwa da ruwan kal.

A wasu lokutan kuma ana amfani da su a miyar dage-dage.