Addinin Kiristanci kawai za a koyar a makaratun Swaziland

Mutum dauke da littafin bible

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sabon tsarin yazo ne bayan mutane sun yi korafi a kan 'yan gudun hijira 'yan Asiya da musulmai da ke kwarara kasar

Gwamnatin kasar Swaziland ta bayar da sabon umarni ga makaratun kasar su rika koyar da addini kirista kawai.

Umarnin dai ya sha suka kuma yana harzuka mabiya wasu addinan a cewar wani rahoto na kamfanin dillancin labaran AFP.

A makon da ya gabata ne ma'aikatar ilimin kasar ta bayar da umarnin ga shugabannin makarantu da su tabbatar da tsarin manhajar karatun bai kunshi wani addini ba illa addinin kirista.

Ya ambato Sahid Matsebula, wani musulmi haifaffen Swaziland wanda ke aiki a wani masallaci da ke kusa da babban birnin Mbabane, yana cewa tsarin zai iya jawo tabarbarewar alaka tsakanin addinai a kasar.

''Wane shiri gwamnati ta tanadar wa yaranmu da ba kiristoci ba? ABin da za a koya musu a makaranta daban da wanda za a koya musu a gida.'' In ji Mista Sahid.

An samar da sabon tsarin ne bayan mutane sun yi korafi a kan yadda Musulmai da 'yan nahiyar Asiya ke kwarara kasar, wanda hakan ya sa majalisar dokoki ta kaddamar da wata hukumar bincike a shekarar da ta gabata.

Stephen Masilela, shi ne shugaban kungiyar coci-coci ta kasar, ya kuma yi maraba da sabon tsarin.

Ya ce, ''addinin kirista shi ne babban addini wanda aka gina kasar nan a kansa."

Masu rubuta sharhi a jaridu sun soki al'amarin.

Kasar Swaziland ba ta da yawan musulmai.

Tuni dai aka mayar da 'yan gudun hijira kasashensu kuma Jabulani Mabuza, ministan kasuwanci da cinikayya ya shaidai wa majalisar kasar cewa nan ba da dadewa ba za a gabatar da dokar da zata tsaurara matakai kan baki wadanda suke so su fara kasuwanci a Swaziland.