Za a yi dokar haramta wa maza furta kalaman sakin aure a Masar

Abdel-Fattah al-Sisi
Bayanan hoto,

Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi zai gabatar da doka a kan saki

Shugaban Masar, Abdel-Fattah al-Sisi - ya bayyana damuwarsa kan ƙaruwar sakin aure a kasar, inda ya bayyana aniyar gabatar da dokar haramtawa maza furta kalaman saki.

Musulmai maza na sakin matansu ne ta hanyar furta "Ki je na sake ki".

A shekara ta 2015, ana sakin mata sau daya cikin ko wane minti hudu a Masar.

Kashi arba'in cikin dari na sakin auren na faruwa ne cikin shekaru biyar din farko da yin aure.

Shugaba Sisi ya ce fitar da dokokin zai bai wa ma'aurata damar sake yin nazari kafin daukar duk wani mataki.

Kawo yanzu dai babu wani martani daga shugabannin addinai na kasar.