Sudan: Dakarun Indonesia sun yi yunkurin ficewa da makamai

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Mahukuntan Sudan na zargin dakarun Indonesiya da yunkurin fasa-kwaurin makamai daga kasar

A makon da ya gabata ne mahukuntan kasar Sudan suka cafke jami'an 'yan sandan Indonesiya masu aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da dama kan zargin yunkurin fasa-kwaurin makamai.

Sun ce dakarun na kokarin ficewa daga kasar da kananan bindigogi 29, da kuma wasu irin bindigogin 70 da suka boye a cikin jakunkunansu.

Gwamnatin Indonesiya na gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa dakarun nata, na yunkurin fita da makaman, lokacin da suke dawowa daga aikin wanzar da zaman lafiya a kasar Sudan.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Indonesiya ya ce sun yi amanna cewa jakunkunan ba na jami'an 'yan sandansu bane, kuma bayanan da suka samu na cin karo da juna.