Iraq: An sake bude makarantu bayan shekaru biyu

(Daga hagu) Heba, Noor, da Janna sun koma aji, bayan sake bude makarantarsu a birnin Mosul (23 January 2017)

Asalin hoton, UNICEF Iraq/2017/Anmar

Bayanan hoto,

'Ya'ya mata da dama ne mayakan IS suka haramtawa ilmi a Mosul

Dubban yaran Iraqi ne ke shirin komawa makaranta a gabashin birnin Mosul, inda dakarun gwamnati suka kakkabe mayakan IS.

Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce makarantu 30 aka bude a ranar Lahadi, inda yara dubu 16 suka koma, bayan shafe shekaru biyu karkashin ikon mayaka masu jihadi.

Ana sa ran sake bude karin wasu makarantun 40 nan da makonni masu zuwa, bayan an kammala binciken nakiyoyi.

Kungiyar IS na amfani da makarantun ne wajen cusa wa kananan yara irin akidarta ta tsattsauran ra'ayinta.

Suna cusawa maza ra'ayi mai tsauri, inda aka cire fannin ilmin zayyane-zayyane, da tarihin kasa, da na falsafa--da mayakan ke dangantawa da kafiri.

Kana dole su haddace ayoyin Alkur'ani mai girma, da kuma halartar horo kan jihadi, da suka hada da yadda za a yi harbi, da dabarun yaki.

Yayinda mata da suka haramtawa samun ilmi a birnin na Mosul- aka saka su yin lullubi , da koyon girki, da share-share, da dai sauran ayyukan da za su taimaki mazajen da za su aura.

Asusun na Unicef ya ce yana goyon bayan mahukuntan Iraqi a yunkurin da suke yi na sake budewa, da gyara makarantun, bayan da aka samu kwanciyar hankali a yankunan.

An lalata gine-ginen da sojoji ke amfani da su yayin fadan.

Asalin hoton, UNICEF Iraq/2017/Anmar

Bayanan hoto,

Asusun Unicef ya ce shekaru biyun da suka gabata ta kasancewa yaran Mosul wani abin firgici

Asalin hoton, UNICEF Iraq/2017/Anmar

Bayanan hoto,

Ahmed, mai shekaru 10, ya shaidawa Unicef: "Yau ji nake kamar na shiga sabuwar rayuwa''

" Bayan shekaru biyu cikin halin firgici, wannan wani muhimmin lokaci ne ga yaran Mosul da suka sake samun 'yanci a fannin ilmi, da kuma fatan da suke yi na samun kyakkyawar makoma'' in ji Peter Hawkins, wakilin Asusun yara na Unicef a kasar Iraqi.

Sauran yara 13,200 da ke zaune a sansanoni a wajen birnin Mosul, wadanda ke cikin mutane 180,000 da suka tsere daga birnin, tun bayan da gwamnati ta kaddamar da farmaki kwanaki 100 da suka gabata, su ma ana taimaka musu kan yadda za su samu ilimi.