An gargadi Zimbabwe kan kwace gidajen mata

HRW ta ce ya kamata gwamnatin Zimbabwe ta dauki matakai

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

HRW ta ce dangi na kwacewa matan da mazansu suka mutu gidajensu a Zimbabwe

Kungiyar kare hakkin biladam da Human Rights Watch ta ce ya kamata gwamnatin Zimbabwe ta hana dangin mazan da suka mutu kwace gidaje daga hannun matansu.

A shekara ta 2013 kasar ta Zimbabwe ta fara amfani sabon kundin tsarin mulkin da ya tanadi 'yancin daidaito ga mata, da suka hada da na mallakar gadon gidaje da filaye.

Amma HRW a rahoton da ta fitar, ta ce a aikace, wannan doka ta shafi matan da aurensu ke cikin rajistar hukuma ne kawai, kuma akalla kashi 70 bisa dari na auren da aka daura a yankunan karkara a gargajiyanci ne, kamar yadda hukumar kula da abinci ta majalisar dinkin duniya ta kididdige.

Kungiyar kare hakkin bil'adamar ta HRW na yin kira ga a aiwatar da wannan doka ga matan da mazajensu suka rasu, amma aurens na su ta hanyar gargajiya ne.

Wasu daga cikin wadanda HRW din ta tattauna da su sun ce surukan nasu sun tilasta musu ficewa daga gidajensu bayan mutuwar mazajensu.

Yayin da wasu ke cewa surukan nasu sun yi barazanar cin zarafi, da wulakanta su, tare da fitar da su daga gidajen nasu da karfin tuwo.

A wasu lokutan 'yan uwan mamatan na nesa kan zo bayan shekaru domin su kwace musu gidajen.