Ban samu nasarar yaki da cin hanci da rashawa ba — Sirleaf

Ellen Johnson Sirleaf shugabar Liberia

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta ce ba a samu nasara a yaki da cin hanci da rashawa a kasar ba

Shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf ta bayyana cewa yakin da take yi da cin hanci da rashawa a kasar bai samu nasara ba.

Yaki da cin hanci da rashawa daya daga cikin manyan alkawuran da ta yi ne a lokacin da aka fara zabenta a shekara at 2005.

Ms Sirleaf ta ce duk da cewa alwashin yaki da cin hanci da rashawar da ta yi bai kai ga nasara ba, amma ba wai saboda cika alkawari bane.

A maimakon haka ta ce dogaro da rashin dogaro da kai, da rashin gaskiya sun yiwa Liberia dabaibayi, saboda shekarun da aka shafe karkashin rashin shugabanci nagari.

Masu sukar shugabar, wacce za ta sauka daga mulki a shekara mai zuwa sun ce ta bar abin fada, tun bayan da ta bai wa 'yan uwanta manyan mukamai.