'Yar Syria ta rubutawa Donald Trump wasika

Bana Al-abed
Bayanan hoto,

Bana da mahaifiyarta Fatima na kasar Turkiyya cikin kwanciyar hankali

Wata yarinya yar kasar Siriya da labarinta ya karade shafukan sada zumunta, saboda yadda ta ke wallafa halin da suke ciki a kasar ta shafin ta na twitter ta rubuta budaddiyar wasika ga shugaban Amurka Donald Trump.

Bana Al-abed 'yar shekara 7 da haihuwa, ta na wallafa labaran halin da birnin Aleppo ke ciki a shafin twitter da taimakon mahaifiyarta.

Mahaifiyarta mai suna Fatima, ta ce Bana ta rubuta wasikar ne a ranar da aka rantsar da Donald Trump a matsayin sabon shugaban Amurka.

A cikin wasikar ta rubuta cewa ''Ni 'yar Siriya ce, anan aka haife ni, kuma iyaye da kakannina duka nan su ke. Mun samu tserewa kudancin birnin Aleppo da aka yi wa kawanya a watan Disambar bara, daga bisani kuma muka kubuta daga kasar inda a halin yanzu muke kasar Turkiyya'', inji ta.

Wasikar ta ci gaba da cewa ''Ina matukar jin dadin sabon wurin da muke rayuwa. Amma fa ina cike da kewar kawaye na, wadanda suka mutu da na raye. Na san yanzu ka zama shugaban Amurka, ko za ka taimakawa 'yan uwana yara 'yan Syria da al'umar kasar?''.

A karshe Bana ta nemi shugaba Trump ya mata alkawarin taimakawa kasar ta, har ta kara da cewa ''Idan ka min alkawarin taimakawa kasa ta, ni kuma zan zama abokiyar ka''.

A lokacin da ya ke yakin neman zabe, shugaba Trump ya bayyana karara zai dakatar da tallafin da Amurka ke baiwa 'yan tawaye da ke yaki da a Syria, amma kuma a kwanakin baya an ji Mista Trump na cewa ya kamata a samu kwanciyar hankali a Syria.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen Rasha, da Turkiyya da kuma Iran suka amince da cimma yarjejeniyar tsagaita wuta ta makonni uku a Syria.