Zargin magudin zabe: Trump na shan caccaka

Shugaba Donald Trump

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Shugaba Trump na ganin kuri'ar wadanda ya kira bakin aure ne ta sa Hillary Clinton ta fi shi yawan kuri'un daidaikun jama'a

Fitattun 'yan jam'iyyar Republic da dama sun caccaki Shugaba Donald Trump na Amurka kan maimaita kalamansa na cewa bai samu yawan kuri'ar jama'a ba ne saboda kusan bakin haure miliyan uku sun yi zaben kasar.

Trump ya ce abokiyar hamayyarsa a zaben Hillary Clinton, ta fi shi da kuri'ar daidaikun jama'a ne saboda wadannan bakin hauren sun yi zabe duk da cewa ba su cancanci kada kuri'a ba.

Dan majalisar dattawa na jam'iyyar Shugaban, Lindsey Graham, ya ce kalaman na Mista Trump ba su dace a ce shugaba ya yi su ba, ba tare da wata sheda ba.

Shi ma kakakin majalisar wakilan Amurkan Paul Ryan, ya ce kamata ya yi Mista Trump, ya yi watsi da wannan zargi da yake yi, maras tushe.

Sanatan Pennsylvania dan jam'iyyar Republic Charlie Dent, shi ma ya soki kalaman na Trump, yana cewa kamata ya yi Shugaban ya dukufa muhimman aikin gwamnati.

Sai dai kakakin shugaban kasar Sean Spicer, ya jaddada cewa, shi dai Mista Trump har yanzu yana kan bakansa kan wannan zargi da yake yi.

Shi dai Mista Trump duk da cewa yawan kuri'ar daidaikun jama'a da ya samu bai kai na Hillary Clinton ba, ya yi nasara ne saboda ya samu mafi yawan kuria'r wakilai, abin da ya ba shi nasara a zaben shugaban kasar.