Ko ka san dalilan da suka sa dan adam ke tafiya da kafa biyu?

Afrika

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Sabanin birrai, mutane sun fi yin tafiya a kan kafafuwa biyu

Burbushin dutse mai launin toka-toka da kasa-kasa da suka watsu a gefen kogin da ya kafe a Arewacin kasar Tanzaniya ta yiwu wasu ne daga cikin sauran alamun da ke nuni da yadda rayuwarmu ta fara a da can.

Curin tokar wutar dutse na nuni da takun tafin kafa iri uku.

Babban ya yi nuni karara yadda ya ja kananan suka yi ta kwane-kwane na tsawon mita 27 (kafa 88) a daukacin falalen da a da toka ce baje.

An same su ne ta hanyar tattakin mutanen farko wadanda suka yi kai-kawo a yankin, kimanin shekara miliyan uku da dari shida da sittin (3.66), kafin samuwar irin rukuninmu, da ake yi wa lakabi da Homo sapiens, da ke tafiya a doron kasa.

Gicciye-gicciyen da ke kan takun na nuni da zaryar takun zomayen da bareyi da kura da goggon biri da gada da mugun dawa.

Wadannan dabbobi dai ruwa da ke kwance a rami ne ya jawo suka tare kusa da wurin.

Sai dai mu yi kintace game da yadda kakannin mutanen da ke gudanar da harkokinsu da har suka bar wadannan alamu a kasa na tsawon miliyoyin shekaru.

Sun yi farautar dabba ko azabtar da dabbobi a ramin da suke shan ruwa, ko kuwa tattaki ne kawai suka yi bayan cin abincin dare?

Amma akwai abin da ke bayyana karara ga duk wanda ya dubi alamun takun.

Ko mene ne wadannan kakannin mutane suka aikata sun yi shi ne suna tafiya a kan kafafuwa biyu.

Asalin hoton, Images of Africa Photobank / Alamy Stock Photo

Bayanan hoto,

Alamun takun sawunkafa wurin Laetoli a Tanzaniya

Alamun sawun kafafuwa da aka tono a Laetoli kusa da kogin Olduvai da ke Tanzaniya, wani wuri ne mai dumbin burbushin duwatsu masu nuni da alamun kakanninmu sun yi tsawon shekaru a da.

Su ne alamun farko da babu tantama cewa kakannin kakanninmu sun sauya takun tafiya daga amfani da kafafu hudu zuwa biyu, ala'amarin da ya mayar da su "masu takun sawu biyu."

Tafiya a mike ta 'yantar da hannnaye suka samu damar dauka da yin amfani da kayan aiki.

Ba a dai gano hakikanin yadda aka yi kakannin kakanninmu suka mike da fara tafiya a kan kafafuwa biyu ba.

Gungun masana kimiyya sun yi sabani kan dalilin da ya sanya mutanen farko suka yi watsi da gudanar da harkokin rayuwa a kan kafafuwa hudu - ko da yake dai akwai alamun yanayin halittu da suka bayyana karara na irin rukunin jinsinmu.

Sai dai, ci gaban da aka samu wajen bincike ya yi karin haske kan dalilin da ya haifar da wannan sauyi.

Fahimtar yadda aka yi muka juya zuwa halittu masu takun sawu biyu a yau zai ba mu amsoshin muhimman tambayoyi da muke da su game da yadda tushen rayuwar rukuninmu ya bijiro.

Tuni aka fahimci cewa rayuwar dindin ta bai wa kakanninmu wasu sababbin damammaki na tabawa da bibiya da aukowa da jifa da koyo.

"Tafiya a mike ta 'yantar da hannaye har su rika dauka da sarrafa kayan aiki," Chris Stringer ya ce, wani babban masani a fannin nazarin dadaddun kayan tarihi da ke gidan Adan a kayan tarihi na kasa Landan. "

Ya bayar da damar yin tafiya mai nisa, kuma da jajircewa wajen gudu.

Hakika, wannan ta yiwu shi ya bude wa kakanninmu kwakwale suka bunkasa."

Asalin hoton, The Natural History Museum / Alamy Stock Photo

Bayanan hoto,

Tafiya a mike ta 'yantar da hannayenmu har muka kera kayan aiki

Irin mutanenmu na farko kakannin kakanninmu an yi kintacen asalinsu guda da gwagggon biri a tsakanin shekaru miliyan 13 da miliyan shida da suka wuce.

Mafi yawan masana kimiyya sun yarda cewa irin wadannan halittun sun yi zama a kan bishiyoyin da suka baibaye Afirka a lokacin.

Abin da kawai muke bukata shi ne mu dubi jariri sabuwar haihuwa don ganin burbushin alamun zama a saman bishiya da aka yi a da.

Sa hannu a kafafuwan jariri nan take za su kanannade kananan yatsu su matse gam.

A saman itatuwa, jariran birai su kan makalkale iyayensu mata da rassan itace tun sa'adda aka haife su.

Idan ba su yi haka ba, za su fado su halaka.

Wannan dadaddiyar mahanga ta yi nuni da cewa sauyin yanayi mabudi ne da ke nuni da hanya.

Kakanninmu sun samu dumbin sauye-sauyen halitta da ta kai ga sun tashi daga tafiya kan kafafu hudu zuwa biyu.

Bangaren cinya da gefen al'aura ya sauya daga sirantar tsawo zuwa fadi tun daga baya, ya kankance, ya zama kamar siffar kwano, inda ya bai wa tsokar jiki damar juya saman duwawu a lokacin da ake tafiya a tsaye.

Lungun da kashin sama ya sauya na nuni da fuskantar ciki, inda ya jawo tafukan kafafunmu suka koma tsakiyar karkashin jikinmu.

Kashin bayanmu ma ya tankware, inda ya yi siffar harafin "S" ta yadda ya taimaka wajen tattara nauyin jikinmu a kan gabar duwawu don sama wa kwakwalwa sauki.

Sai kawai kafarmu ta kara tsawo, al'amarin da ke ba mu damar yin babban motsi da dogon taku.

Tafukan sawunmu su ma sun sauya.

Birai na da tsawon sawu, mai manyan yatsun kafa da ke harde rassan itace.

Yatsun kafar mutane gajeru ne, kuma sun jeru wani na bin wani suka samar da mariki a karshen taku

Ta yaya kuma wane dalili ya haifar da wadannan sauye-sauye?

Asalin hoton, Steffen Foerster / Alamy Stock Photo

Bayanan hoto,

Tafukan gwaggon biri an tsara su ne yadda za su iya makalkale abu, amma ba don tafiya ba

Wannan mahanga ta tsawon zamani ta yi nuni da cewa sauyin yanayi jigo ne wajen fahimtar yadda al'amarin yake.

Miliyoyin shekaru da suka shude, Afirka ta fara asarar dazukanta masu dimbin tsirran ciyayi da suka girma, ta haka kakanninmu suka fara yin kaura daga wurin zamansu a dazuka, suka tare a wuri mai bishiyoyi da ciyayi, ta yadda za a hango dabbobin da ke farautar nama.

Yin taku da sawu biyu ya yi matukar dacewa da muhallin da ke da karancin bishiyoyi.

Tsayuwa tsaf zai ba ka damar ganin tsawon ciyawa da kakanninmu wadanda suka samu tsayawa tsaf ta yiwu sun rayu ne har sun baza kwayoyin halittarsu, don haka za a iya fahimta cikin sauki yadda al'amarin ya kasance daga tsayuwa zuwa tafiya ta dindindin kai tsaye.

Yanayin Afirka bai yi bushewar da ta haifar da yankin itatuwa da tsirrai na 'sabana' har sai da rukunin mutanen farko suka bayyana, wadanda a Turancin kimiyya ake yi wa lakabi da aka samu Sahelanthropus and Orrorin.

Burbushin duwatsu sun yi nuni da cewa tafiya kan kafafuwa biyu ya faru ne a farkon samuwarmu.

Misali, burbushin duwatsun kokon kan mutum an gano su a Chadi, yankin Afirka ta Tsakiya a tsakanin shekarun 2001 da 2002.

Kokon kai mai siffa irin na biri na asalin mutanen farko ne da ake yi wa lakabi da Sahelanthropus tchadensis, sun kuma rayu a tsakanin shekaru miliyan bakwai zuwa shida da suka shude.

Cikin kokon ya yi nunin shigewar wuya a ciki a tsaye, kamar yadda namu yake, sabanin yadda gwaggon-biri da yake kwance.

A cewar wadanda suka gano lamarin, wannan na nuni da cewa mutanen farko "Sahelanthropus" ta yiwu sun yi tafiya a mike kan kafafuwa biyu.

Idan mutanen farko da suka gushe ba su yi ba, wani rukunin na gwaggon biri da suka rayu shekaru miliyan shida da suka wuce ta yiwu sun yi.

Wannan rukuni na dabbobi, da ake yi wa lakabi da Orrorin tugenensis sun siffantu da kashin kafa irin na mutanen wannan zamani, al'amarin da ya nuna cewa sun yi tafiya a mike.

Amma akwai matsala tattare da manhangar yanki mai ciyayi da itatuwa (savannah).

Mafi bayyana karara, yanayin Afirka bai yi bushewar da zai haifar da wuri mai ciyawa da bishiyoyi jefi-jefi na sabana, har sai da rukunin mutanen farko (Sahelanthropus and Orrorin) suka bazu a doron kasa.

Asalin hoton, Sabena Jane Blackbird / Alamy Stock Photo

Bayanan hoto,

Kokon kan mutumin rukunin farko (Sahelanthropus)

A gaskiya, yanayin Afirka ya samu sauye-sauye sanadiyyar samuwar mutane, al'amarin da ko wanne ya sauya tsirran da ke doron kasa.

Babu wani abu karara da ya haifar da sauyin dindindin da ya ingiza sauyin rayuwa daga tafiya bisa kafafu hudu zuwa biyu.

Wadannan gwaggon birai su kan shiga cikin dajin da ke lullube da bishiyoyi su yi tafiya a tsakanin rassan itatuwa da kafufuwa biyu.

Sannan akwai wata babbar matsala da ta ki ci, ta ki cinyewa.

Mene ne dalilin da ya sanya sauran halittu suka fi son zama a yankin tsirrai da itatuwa tare da yin tafiya a kan kafafuwa hudu?

Akwai ma nau'ukan birrai da suka shafe tsawon lokacinsu a cikin ciyayi, kamar gwaggon biri, amma har yanzu suna tafiya ne a kan kafafuwa hudu.

A karshe, akwai wani muhimmin al'amari game da wadannan buraguzan alamun duwatsu na mutanen farko kakannin kakanninmu masu tafiya da kafafuwa biyu.

An fi samunsu a burbushin duwatsun daji mai bishiyoyi da dabbobi.

"Wannan lamari ya saba wa fahimta, amma ta yiwu dabi'ar ta samo asali ne daga cikin itatuwa," inji Stringer.

Bibiyar harkokin manyan birran Sumatra (Indonesiya) ya bayyana cewa, nau'ukan gwaggon biri na tafiya a daji kan bishiyoyi ne ta hanyar taka rassa da kafafuwa biyu, inda suke amfani da hannayensu wajen rike abin da zai tarairayi nauyinsu.

Wannan na taimaka musu su yi tafiya a kan rassa masu siranta maimakon jibga nauyin gwagon biri in ya yi amfani da kafafuwa hudu, ta yadda hakan ke ba su damar kai wa ga 'ya'yan itace, su kuma tsallaka daga wannan bishiya zuwa waccan.

Asalin hoton, dbimages / Alamy Stock Photo

Bayanan hoto,

Gwaggon birin (Orangutans) na tafiya kan rassan itatuwa da tafin kafarsu

Kakannin mutane sun yanke alaka tsakaninsu da manyan birrai kimanin shekaru miliyan 10 da suka wuce, amma duk da haka manyan biran orangutans suna da kokon gwiwa mai kama da na mutanen zamani.

A cewar Robin Cromton, wani masanin dadaddun al'amura daga Jami'ar Liverpool, da Susannah Thorpe masani kan rayuwar gwaggon biri daga Jami'ar Birmingham, sun yi nuni da cewa asalin tafiya kan kafafuwa biyu tushensa na da nisa fiye da yadda aka dauka a da.

"Rukunin mutanen farko (Orrorin) ya nuna cewa sun siffantu da dabi'un da suka ba ni tabbacin cewa sun yi daidai da masu zama a kan bishiya, wadanda hannu ke taimaka musu wajen tafiya bisa kafafuwa biyu yadda muka yi hasashe," kamar yadda yake kunshe a bayanin Cromptom

Akwai wani muhimmin al'amari da ba a yi la'akari da shi ba, a tsakiyar tafiyarmu don kai wa ga yadda tsarin tafiya bisa kafafuwa yake.

Mahangar nazari da ta samu karbuwa, amma ita ma daya ce daga cikin yawan-yawan dabarun nazari da aka yi amfani da su wajen bayyana dalilin da ya sanya kakanninmu suka mike tsaye bisa kafafuwa biyu.

Wasu masu binciken suna ganin cewa tafiya a mike ya taimaka wa kakanninmu su fake a wuri mai sanyi a yanayin zafin Afirka lokacin da ake rana.

Wata garabasar, wannan dabara ta yiwu ta taimaka wajen bayyana dalilin da ya sanya kakanninmu suka yi asarar gashin jikinsu suka koma masu tsurar fata.

Tsayuwa na nufin saman jiki kawai za a lullube da gashi don kariya daga rana, amma asarar gashin jiki zai bai wa fata damar tsanewa daga jikar yayyafi ko iska.

An yi ta takaddama kan hakikanin lokacin da wadannan siffofin suka bayyana a lokacin samuwar dan Adam da karfin ikon da ya bijiro masa, har ake tunanin al'amarin ya faru ne ga kakanninmu tashin farko har ya ingiza su zuwa yin tafiya bisa kafa biyu.

Amma akwai binciken baya-bayan nan da ya yi nuni da cewa akwai muhimmin al'amari da aka ki yin la'akari da shi, wanda shi ne matakin da ke tsaka-tsaki wajen kai wa ga tsarin tafiya kan kafafuwa biyu.

Kuma wannan abu hujja ce game da takun sawayen da aka samu a kasar Tanzaniya.

Asalin hoton, Danita Delimont / Alamy Stock Photo

Bayanan hoto,

Kyautatuwar "Lucy" nau'in biri mai siffar sawun gwaggon biri da na mutane

Wasu masu binciken na amfani da fasahar zayyanar kwamfuta ta 3D wajen gyaran fasalin wasu jinsi, domin abin na iya yiwuwa idan an yi nazari tsohon tarihin takun sawun da suka bari.

Idan muka hada wannan da abin da muka sani game da tsarin jikin mutum ya bai wa masana kimiyya damar samun cikakken bayani tsakanin tafiya da kakanninmu na farko da kuma yadda muke yin tafiya a yau.

Binciken kwanan nan iri biyu da aka gudanar sun yi amfani da wannan hanya wajen nazarin takun sawun Laetoli.

Tambarin sawun an dauka na daidaiku ne a rukunin jinsi guda a matsayin shahararrun gwaggon biri Lucy mai siffar takun sawun mutum da na biri, wanda nau'ukansa suka kare (Australopithecus afarensis).

Sun rayu ne a tsakanin shekaru miliyan uku da dubu 900 zuwa miliyan biyu da dubu 900 da suka wuce, irin wannan jinsi ana sa ran sun hadu da sauye-sauyen jiki da suka bai wa kakanninmu damar yin tafiya a mike, ko da a ce har yanzu za a dan sha wuya kafin a yi tafiya kamar yadda za mu gano yadda lamarin ya faru.

Ta yi fama da dimbin karayar kashi kafin mutuwarta wanda ake ganin ya yi daidai da fadowa daga wuri mai nisa.

Daya daga nazarin da masu binciken suka gudanar a cibiyar Faruwar dadaddun al'amura ta Max Plank da Gidan kayan tarihin halittu na Amurka, ya yi nuni da cewa Lucy sun yi wata irin tafiya da ta dan bambanta da wadda aka saba gani.

"Alama ba ta bayyana ba, kan cewa ko sun yi wani salon tafiyar da ta bambanta da ta mutanen zamani, amma alamun sawun Laaetoli har yanzu ya nuna akwai wasu bambance-bambancen da, da sun kara kaimi da wahalar tafiya da kafafuwa ga wadanda suka yi su," a cewar Kevin Hatala na Cibiyar nazarin tarihin dadaddun abubuwa, wanda ya jagoranci masu binciken.

A nan labarin ya kara haifar da rudani.

Wani sabon nazari da aka gudanar kan kwarangwal din Lucy, sannan aka wallafa shi a Agustan 2016, ya yi nuni da cewa ta yi fama da dimbin karaya kafin ta mutu, al'amarin da ya yi daidai da fadowa daga wani wuri mai nisa.

Binciken wanda gungun masu aikin suka wallafa cikin watan Nuwamba a shekara ta 2016 ya yi nuni da cewa nau'ukan birin a afarensis ya shafe tsawon lokacin yana hawan bishiyoyi.

Wani sabon binciken da aka dauki wata mahangar daban na nuni da cewa Lucy ta kasance mai hawan tsauni ce.

Asalin hoton, Fabio lamanna / Alamy Stock Photo

Bayanan hoto,

Tagwayen tsaunukan Habasha, inda nau'ukan mutanen farko suka zauna

"Al'amarin zai yi sauki, idan aka yi magana kan faruwar halittu, tunda tuni biri ya saba da hawan tsaunuka zuwa yin zarya a hanya mai gurji-gurji, inda ya ke ta tsalle a tsakaninsu, a hankali sai ya shafe tsawon lokaci a kasa, sannan ya shafe wasu lokuta a falelen dutse, fiye da yadda nau'in gwaggon biri guda zai shafe yana tafiya a kan falelen dutse," a cewar Isabelle Winder, wani masanin burbushin rayuwar halittu a burbushin duwatsu dauke da alamu, daga Jami'ar New York.

A wata makala da aka wallafa a shekara 2015, Winder da abokan aikinta sun yi nuni da cewa ta yiwu sauye-sauyen da aka samu a doron kasa suka yi tasirin juyar da kakanninmu suka zama masu tafiya a kan kafafuwa biyu.

Masu binciken sun nuna cewa wasu sassan gabashin Afirka, inda aka samu mafi yawan alamun burbushin duwatsun kakanninmu har yanzu suna motsawa.

Sun zauna a wani wuri mai yamutsi da ke tsaunukan gabar kogi, wadannan kakannin mutane sun zauna a yanayin rashin natsuwa, mai tudu da kwarin hawa da sauka.

"Ina ganin da rashin natsuwa da kyawun hanyar kasa, kuma kafafunmu na nuni da haka," a cewar Matthew Benneth, masanin dadaddun al'amura daga Jami'ar Bouremouth.

Gabashin Afirka na da dimbin tudun zaftarewar kasa da bullukowar tsirrai da ke bayar da mafaka daga dabbobi masu cin naman mutane, tare da kariya a wuraren kwanciyar barci," inji shi.

Aikin da Bennet ya gudanar ya mayar da hankali kacokam kan nazarin takun sawun mutum da ya kwatanta shi da tafin kafafuwan kakanninmu.

Ya yi amfani da fasahar zayyanar kwamfuta ta 3D da ya kirkiro bisa doron sawun da ya samu a Laetoli da sauran wurare da suka hada da Ileret a Kenya, da nisan shekarunsu ya kai miliyan daya da rabi da suka wuce.

Nau'ukan fasalin na nuni da cewa rukunin halittun sun yi tafiya da kaikawo kamar yadda muke yi a yau.

Asalin hoton, BBC Sport

Bayanan hoto,

Sabanin birrai, mutane sun fi yin tafiya a kan kafafuwa biyu

Bernnets ya tabbatar da cewa kafar mutum na da saukin juyawa fiye da yadda ake zato, ta yiwu saboda muna kunshe tamu a cikin takalma.

Takun sawun kafarmu bai bambanta daga kafafuwan da suka yi wadannan alamun sawu fiye da shekaru miliyan uku da suka wuce ba.

"Muna ganin sawun kafa abin juyi ne da ke ba mu damar dagawa da jefa kafa a yayin tafiya," inji shi.

"Wannan aiki ne mai matukar saukin yi.

Muna da saukin juya kafarmu da ke ba mu damar jera abubuwa.

"Za ka iya takun hawan bishiya in kana bukata, za ka iya fakewa a gangaren tsauni, ko ka iya ci gaba a lokacin da kake motsawa daga mabubbugar ruwa zuwa wani fili mai santsi.

Duk da cewa gogaggen zane-zanen alamun karkataccciyar hanya irin ta Laetoli da ke da shaida kakkarfa da ke danganta mu da kakanninmu na farko, kuma ta yiwu su bayyana cewa kafafuwanmu ba su bambanta da na mutanen da suka yi alamun sawunsu fiye da shekara miliyan uku da suka wuce ba.

Shiga jerin mutane fiye da miliyan shida da ke son shafin doron kasa na BBC, ta hanyar taba maballin kauna a shafinmu na Facebook da kuma bin mu a shafinmu na twitter da instagram..