Wata 'yar kunar-bakin-wake ta rungumi wani mutum a Maiduguri

Maiduguri
Bayanan hoto,

A kwanakin nan hare-haren kunar bakin wake na karuwa a birnin na Maiduguri

A kalla mutum uku ne aka kashe a wasu hare-haren kunar-bakin-wake da aka kai da safiyar ranar Laraba a Maiduguri babban birnin jihar Borno a Najeriya.

Wannan dai na zuwa ne kimanin makwanni biyu da kai hari jami'ar birnin, inda mutum hudu suka rasa rayukansu ciki har da wani Farfesa.

Wani jami'in bayar da agaji ya shaida wa BBC cewar macen farko ta yi hakon gidan wani dan banga ne wanda aka sani da yin bincike a kan motoci a manyan hanyoyin birnin.

Sai 'yar kunar bakin waken ta kwankwasa kofar gidan dan bangar, wanda rahotannin suka ce ya ki bude wa.

Daga nan ne ta yi maza ta rungumi wani mutum da ke kan hanyarsa ta zauwa masallaci kuma ta tayar da bam din da ta yi damara da shi.

Nan take dukkan mutanen biyu suka mutu.

Sai dai mutumin da ya kai hari na biyun bai samu ya kai ga babban masallacin unguwar Kaleri ba saboda an hanashi zuwa wurin.

Abin da ya sa ya mutu shi kadai tare da raunata mutum biyu bayan da bam din da yake dauke da shi ya tashi.

Babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin, amma dai kungiyar Boko Haram ta yi kaurin suna wurin amfani da mata 'yan kunar bakin wake domin kai hare-hare.