Netherland za ta taimaka wa masu son zubar da ciki

Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Trump ya hana bai wa kungiyoyi da ke bayar da tallafi ga masu zubar da ciki kudi

Gwamnatin Holland ta ce za ta kafa asusun kasashen duniya domin magance matsalar da ka iya aukuwa sakamako dadakatar da kudaden agaji da Donald Trump ya yi ga kungiyoyin da ke bayar da tallafi wajen zubar da ciki a kasashe masu tasowa kamar yadda Donald Trump ya bayyana.

Ministan ci gaban kasar, Lilianne Ploumen, ya ce ba za'a bari shawarar da shugaba Trump ya yanke ya rusa ci gaban kiwon lafiyar mata ba.

Ta ce janye kudade ba zai rage yawar zubar da ciki da ake yi ba, amma zai kara hadarin da mata ke fuskanta wurin zubar da ciki ya kuma zama sanadiyar karuwar mace macen mata masu juna biyu.

A ranar Litinin ne Mista Trump ya sanya hannu a kan dokar dake jaddada hana Amurka ta baiwa kungiyoyin kasashen duniya dake yi ko tattaunawa kan zubar da ciki a matsayin wani zabi na tsarin iyali.

Hukumar Lafiya ta duniya ta yi kiyasin cewa mata miliyan 22 ne ke fuskantar matsala wajen zubar da ciki a ko wace shekara, akasarinsu na kasashe masu tasowa.