Somalia: Al-shabab ta hallaka mutane a wani harin otal

wadanda da harin ya ritsa da su

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Wadanda suka tsira daga harin sun bayyana yadda mutanen da ke zaune0. a Otel din suka rika buya a karshin gado kuma wasu suka rika dira daga tagar domin su tsira da ransu

Mutum 10 sun mutu kuma sama da 50 sun jikkata bayan wata mota dauke da bam da kuma wasu 'yan bindigia sun kai hari a wani otal a Magadishu babban birnin Somaliya.

A ranar Laraba ne dai 'yan sanda suka ce harin ya auku ne a otal din Dayah, inda ake zato wasu 'yan majalisar kasar ke zaune.

Ministan tsaron kasar, Abdurazak Omar Mohamed ya ce jami'an tsaron sun kashe maharan su hudu.

Kungiyar Al-shabab ta dauki alhakin kai harin.

Masu kula da motar daukar marasa lafiya sun ce sun ga gawarwaki 28 a otal din kuma wasu mutum 43 sun jikkata ciki har da 'yan jarida bakwai.

Har yanzu dai ba a tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba a hukumance.

Wasu ganau sun ce maharan sun yi amfani da mota makare da bama-bamai domin su fara kai harin a hanyarsu ta zuwa otal din kuma suna shiga ciki suka fara harbi.

Lokaci kadan bayan tashin bam din farko sai wani bam din ya sake tashi a wata motar inda mutane da dama wadanda suka taru a wurin suka jikkata.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da kungiyar Al-shabba ke kai hari otal ba, musamman wanda 'yan majalisar dokokin kasar ke yawan taruwa.