'Yar Micheal Jackson ta ce kashe babanta aka yi

Paris Jackson da Micheal Jackson

Asalin hoton, Google

Bayanan hoto,

Paris tana da shekara 11 a lokacin da mahaifinta ya mutu ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2009

Paris Jackson 'yar shahararren mawakin nan Micheal Jackson ta ce ta yi amanna kashe Babanta aka yi.

A wata doguwar hira da ta yi da mujallar Rolling stone, ta ce ta gamsu cewa, mutuwar mahaifinta a shekarar 2009 wani abu ne da aka shirya.

Mawakin dai ya mutu ne sanadiyar allurar kashe zafi na propofol da aka yi masa ta wuce yawan da ya kamata a yi. Daga bisani kuma aka kama likitansa Conrad Murray da laifin kisan kai ba da gangan ba.

Amma Paris tana ganin cewa akwai sauran rina a kaba.

Ta ce, ''ya kan nuna alamun cewa wasu mutane na so su kai masa hari.''

Ta kara da cewa akwai lokacin da ya ce, "watarana za su kashe ni".

A lokacin da Brian Hiatt wanda ke yin hira da ita ya tambaye ta ko ta na ganin kashe mahaifinta a ka yi? Sai Paris 'yar shekara 18 ta ce, "babu shakka".

Ta ci gaba da cewa mutane da dama sun so mutuwar mahaifina kuma za ta yi iya kokarinta domin tabbatar da cewa an yi musu hukuncin da ya dace da su.

Matashiyar ba ta ambato takamaimai sunayen mutanen ba kuma ba ta ambato Conrad Murray a zargin da take yi ba.