Trump ya umarci a fara katange Amurka daga Mexico

Donald Trump

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaba Trump ya ce zai cika alkawarin da ya yi a lokacin yakin neman zabe

Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanya hannu kan kudurin da zai bayar da dama a fara gina kantanga a kan iyakar kasar da kudancin Mexico.

Ya umarci a fara hana kudade isa ga wasu biranen Amurka da ke faran-faran da bakin haure.

A wata hira da kafar yada labarai ta ABC, Mista Trump ya ce kasar Mexico ce za ta biya ta kudin da za ta kashe wajen gina katangar.

Amma ya ce daga farko Amurka ce za ta dauki nauyin aikin, kafin daga baya Mexico ta mayar mata da kudinta.

Gina katangar mai tsayin mil 2,000 na daya daga cikin muhimman alkawuran da ya yi a lokacin da yake yakin neman zabe.

A wurin wani taro a ma'aikatar tsaron kasa, Shugaba Trump ya kara da cewa "Tun da fari muke magana a kan wannan batu," inda ya bayar da karin wasu umarnin.

Ana san ran zai saka hannu kan wasu dokokin shige da fice da kuma tsaron kan iyaka a cikin wannan makon.

Al'ummar Mexico na ganin gina katangar a matsayin nuna banbancin launin fata.

Kuma shugaban kasar ya sha nanata cewa kasarsa ba za ta biya kudin aikin ba.