Libya: An kwace yankin Benghazi daga masu ikirarin Jihadi

Dauki-ba-dadin Ganfouda ta haddasa asara sosai

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Kama yankin na Ganfouda babban koma-baya ne ga mayaka masu alaka da IS da Al Qaeda

Kakakin rundunar sojan sa-kai da ke iko da gabashin Libya, ya ce sun kame gundumar Ganfouda, wadda ke Benghazi, birni na biyu mafi girma a kasar, daga mayaka masu ikirarin Jihadi.

Yankin shi ne daya daga cikin yankuna na karshe da ake fafata yaki a cikinsu a birnin na biyu mafi girma a Libya.

Wannan gunduma ta ga artabu mafi muni tsakanin mayakan da Field Marshal Khalifa Hefter ke jagoranta, da gamayyar sojan sa-kai 'yan yankin masu ikirarin Jihadi, wadanda suka hada da masu alaka da kungiyar IS da Al Qaeda.

Tsawon watanni gundumar Ganfouda wadda aka yi wa kawanya, kusan an yanke ta daga sauran yankunan birnin na Benghazi, sakamakon shingayen da dakarun da ke biyayya ga Field Marshal Khalifa Hefter suka kakkafa.

Kakakin sojojin yankin gabashin Libyar, ya ce a yanzu sun 'yanto gundumar, sai dai kuma wasau daga cikin 'yan gwagwarmayar sun tsere zuwa wani yanki da ke kusa, wanda ake wa lakabi da ''12 blocks''.

Idan dai har wannan nasara da ya ayyana ta tabbata kuma ta dore, to hakan ba karamin cigaba ba ne ga dakarunsu.

Yakin da aka yi sama da shekara biyu ana fafatawa a birnin na biyu mafi girma na Libya, ya haifar da asara sosai, domin yaki ne da ya yi muni, ga kuma dubban mutanen da ya raba da muhallinsu.

Mazauna birnin sun ce har yanzu sojan sa-kai masu ikirarin Jihadi ne ke iko da wasu sassan tsakiyar birnin na Benghazi, duk da cewa ba wani artabu da ake samu a 'yan kwanakin nan.

Dauki-ba-dadin da aka yi ta yi kan kokarin kama iko da gundumar ta Ganfouda ta ritsa da farar hula da dama tsawon watanni, inda suka kasance ba su da wata mafita.

Da dama daga cikinsu sun sheda wa kungiyoyin kare hakkin dan adam cewa suna jin tsoron guduwa, saboda sojoji suna kama mazajen cikinsu bisa zargin cewa suna taimaka wa mayakan sa-kai masu ikirarin Jihadi.

Su ma sojojin sun yi ikirarin cewa mayakan sa-kai na garkuwa da wasu iyalan.