Ta'addanci: Trump zai dawo da azabtarwa don tatsar bayanai

Sojin Amurka na azabtarwa da ruwa

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojojin Amurka na amfani da ruwa wajen azabtarwa domin tatsar bayanai

Shugaba Donald Trump ya ce ya yi amanna gana akuba ko azabtarwa na da tasiri wajen tatsar bayanai daga wadanda ake zargi da ta'addanci.

Sai dai Shugaban ya ce zai mika maganar ga sakataren tsaro da kuma darektan hukumar leken asiri ta Amurka, CIA, kan ko ya kamata a dawo da tsarin amfani da azabtarwar.

A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta ABC, Mista Trump, ya ce, wajibi ne Amurka ta yaki wuta da wuta, kan irin muguntar da kungiyar IS ke yi a Gabas ta Tsakiya.

Shugaban ya yi kalaman ne, yayin da rahotanni ke nuna cewa gwamnatinsa na duba yuwuwar sake dawo da gidajen yari na sirri na hukumar CIA, a kasashen waje.

Shugaba Obama ya haramta amfani da tsarin gana akuba, ta hanyar nutsar da wadanda ake neman bayanai a wurinsu a cikin ruwa, bayan da gwamnatin Bush ta rika amfani da tsarin kan wadanda ake zargi da ta'addanci.