Gambia: Shugaba Adama Barrow zai koma kasarsa

Adama Barrow yana da farin jini wajen matasa

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Adama Barrow, wanda mai hada-hadar gidaje ne, ya taba aikin gadi a wani kanti a Landan

Jami'an gwamnatin shugaba Adama Barrow na Gambia sun sanar da cewa a ranar Alhamis din nan ne shugaban zai koma kasar daga Senegal, inda aka rantsar da shi a makon da ya wuce.

Sabon shugaban ya ci gaba da zama a mawkabciyar kasar tasa ne, a yayin da shugabannin kasashen yammacin Afirka suka shawo kan tsohon shugaba Yahya Jammeh ya sauka daga mulki.

Jami'an diflomasiyya ne suka bukaci Mista Barrow ya gaggauta komawa Gambiar domin gudun barin kasar ba shugaban.

Wasu rahotanni sun ce Mista Barrow zai fara zama ne a gidansa, yayin da ake tantance gidan shugaban kasa don gudun duk wani hadari ko matsala bayan ficewar Yahya Jammeh zuwa gudun hijira a Equatorial Guinea.

A bangare guda dubban sojojin kungiyar ECOWAS na cigaba da zama a kasar dan tabbatar da tsaro, sakamakon rahotanin da ke cewa akwai tarin 'yan gani-kashenin Yahya Jameh a cikin jami'an tsaron kasar.

Jakadan majalisar dinkin duniya a yammacin Afirka Muhammad Ibn Chambas, wanda ya ce majalisar za ta taimaka wajen tabbatar da tsaro a Gambiar shi ne zai raka Shugaba Barrow.