Za a taimaka wa Nigeria kan harkar man fetur da lantarki

Yawancin matatun man Najeriya sun lalace, hakan ta sa wasu ke ganin kamata ya yi gwamnati ta gina sababbi maimakon yi wa tsofaffin kwaskwarima
Wani fitaccen kamfanin na duniya mai suna General Electric ya nuna aniyarsa ta zuba hannun jari a matatun mai a Nigeria.
Kamfanin zai tallafa wajen farfado da matatun man fetur da ke neman durkushewa domin inganta harkokin samar da tataccen man fetur da wutar lantarki a Najeriyar.
Wasu masana tattalin arzikin dai na ganin zai fi alfanu ga gwamnatin kasar ta gina wasu sabbin matatun mai a maimakon dogaro da tsaffin da ba a san makomar su ba.
Batun tabarbarewar tsaro a yankin Naija Delta mai arzikin mai, na daga cikin batutuwan da aka nuna damuwa kai.
To sai dai kuma mai magana da yawun kamfanin mai na kasa wato NNPC, ya ce tuni aka shawo kan wannan matsala kuma ayyukan tsagerun Naija Delta sun yi sauki a yankin.
Tattalin arzikin Najeriya dai ya shiga mawuyacin hali, tun bayan faduwar danyan mai a kasuwannin duniya wanda kasar ta dogara da shi wajen samun kudaden shiga.