Fitacciyar marubuciya Buchi Emecheta ta mutu

Buchi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Buchi Emecheta ta shahara wajen kare hakkin mata

Fitacciyar marubuciyar nan 'yar Najeriya Buchi Emecheta ta mutu.

Ta rasu ne a gidanta da ke birnin London tana da shekara 72.

Buchi Emecheta ta rubuta littafai fiye da ashirin a kan fannoni daban-daban, koda yake ta fi mayar da hankali kan 'yancin mata da irin fafutikar da suke yi.

Wasu daga cikin littafanta su ne: 'The Joys of Motherhood', 'Second-Class Citizen', 'The Bride Price' da kuma 'The Slave Girl'.

Buchi Emecheta ta samu lambobin yabo da dama game da rawar da ta taka wajen bunkasa rubutun kagaggun labarai.

An haife ta a birnin Lagos ranar 21 ga watan Yulin shekarar 1944, amma ta kwashe yawancin rayuwarta a London.