Venus da Serena Williams za su fafata a Australian Open

Serena

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Serena ta dade tana jan zarenta

Venus Williams ta 'yar uwarta Serena Williams za su fafata a wasan karshe na cin kofin Grand Slam a karo na tara a Melbourne bayan dukkanin su sun yi nasarar kai wa matakin kusa da na karshe a gasar Australian Open.

Venus, mai shekara 36, ta doke Coco Vandeweghe 6-7 (3-7) 6-2 6-3 inda ta kai matakin karshe a karon farko tun shekarar 2009.

Ita kuwa mai matsayi na biyu a gasar Tennis ta duniya Serena, 'yar shekara 35, ta buge Mirjana Lucic-Baroni 6-2 6-1 a zagaye na biyu na wasan kusa da na karshe.

Serena na kokarin lashe Grand Slam na 'yan ɗai-ɗai a zagaye na 23.

Asalin hoton, EPA

Bayanan hoto,

Rabon Venus ta ci Grand Slam tun shekarar2008

Kazalika wannan ne zai zamo karo na bakwai da Serena za ta dauki kofin Australian Open, yayin da ita kuma Venus ke fatan daukar wani baban kofi karo na takwas, kuma karon farko a Melbourne tun lokacin da ta lashe Wimbledon a 2008.

Bayan ta kai matakin kusa da karshe, Venus Williams, ta ce "Yadda Serena ke buga wasan tennis abin al'ajabi ne. Babban burina shi ne na kara da ita ranar Asabar."