Mark Zuckerberg ya ce bai zai nemi shugabancin Amurka ba

Mark Zuckerberg

Asalin hoton, Reuters

Shugaban kamfanin sada zumunta na Facebook Mark Zuckerberg ya ce ba zai nemi takarar shugabancin Amurka ba.

Lokacin da shafin Buzzfeed News ya tambaye shi kan batun, Mark ya ce: "A'a, na mayar da hankalina ne kan kamfanin Facebook da kuma bunkasa gidauniyata ta Chan Zuckerberg Initiative."

An yi ta rade-radin cewa watakila Mr Zuckerberg zai tsaya takarar shugaban Amurka nan gaba bayan ya yi wasu kalamai na siyasa sannan ya bayyana cewa zai yi ran-gadi zuwa dukkan jihohin kasar.

Mark, mai shekara 32, yana da 'yancin tsayawa takarar shugabancin kasar a shekarar 2020.

Asalin hoton, vanity fair

Bayanan hoto,

Ana ta rade-radin cewa Mr Zuckerberg zai tsaya takara

A watan Afrilun shekarar 2016, jaridar Fortune ta ruwaito cewa Facebook ya amince ya sauya tsarinsa ta yadda Mr Zuckerberg zai samu damar tsayawa takara.

Mamallakin na Facebook ya sassauta ra'ayinsa game da addinin, yana mai cewa addini "abu ne mai matukar muhimmanci" a lokacin Kirsimetin da ya wuce.

A baya dai Mr Zuckerberg ya bayyana kansa a matsayin mutumin da ba shi da addini, abin da ake gani ya sanya wasu Amurkawa ba sa jituwa da shi.