Arsene Wenger 'zai amince' da tuhumar da FA ke yi masa kan rashin kan da'a

Arsenal manager Arsene Wenger (centre) is sent to the stands by referee Jon Moss during the game against Burnley

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kori kocin Arsenal Arsene Wenger daga wurin da kociya ke tsayawa lokacin wasan su da Burnley

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya ce zai amince da tuhumar da hukumar kula da kwallon kafar Ingila, FA ke yi masa kan rashin da'a lokacin wasan lig din da suka doke Burnley da ci 2-1.

An tuhumi Wenger, mai shekara 67, da laifin zagi da kuma tunkude jami'in wasa Anthony Taylor bayan an kore shi daga fili ana dab da kammala wasan.

An kore shi ne saboda martanin da ya yi cikin fushi bayan an bai wa Burnley bugun fenareti a minti na 93.

Wenger, wanda daga baya ya nemi afuwa, ya ce zai nemi FA ta ba shi damar kare kansa.

Ya kara da cewa, "Na riga na fadi abin da zan ce. Ban sani ba ko za a hukunta ni ko kuma irin hukuncin da za a yanke min."

A cewarsa, "Abin da kawai zan ce shi ne na yi mamakin korar da aka yi min."

Bayan alkalin wasa Jon Moss ya kore shi, Wenger ya fice daga filin amma ya tsaya a kofar shiga filin wasan sanna ya ki fita inda ya rika kallon ragowar wasan.

A lokacin da Taylor ya shaida masa ya matsa daga wurin, an ga Wenger yana ture shi.

Amma da aka tambaye shi ko zai amince da tuhumar da ake yi masa, sai Wenger ya ce: "Eh. Zan iya kare kaina kan duk zargin daake yi mini."