Za a yi wa miliyoyin yara riga-kafin kyanda a Nigeria

Ma'aikatan kiwon lafiya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Yara sama da 100 ne suka mutu saboda kyanda a bara

Kimanin yara miliyan hudu ne za a yi wa allurar riga-kafin cutar kyanda a wani shiri na majalisar dinkin duniya a Najeriya.

Akalla yara 100 ne suka mutu a bara sakamakon cutar ta kyanda.

Asusun yara na majalisar, Unicef, ne ke aiwatar da shirin a jihohin Adamawa da Borno da Yobe inda rikicin Boko Haram yafi shafa.

Rashin tsaro a yankin dai ya kawo cikas a kokarin da ake yi wajen yin riga kafin.

A bara an samu yara 25,000 masu fama da kyanda a Najeriya kuma kashi 97 cikin 100 na masu dauke da cutar yara ne da 'yan kasa dashekara 10.

"An samu cigaba a harkar tsaro don haka ne muke so mu yi amfani da damar domin mu kai ga wuraren da a baya ba za mu iya zuwa ba domin mu kare yaran daga yaduwar cutar mai hadarin gaske" a cewar Mohamed Fall, babban jami'in hukumar.

Ya kara da cewa "Mun damu matuka a kan yaran da ke zaune a yankunan jihar Borno da har yanzu ba mu kai gare su ba".

Ana samun karuwar yaduwar cutar kyanda ne a farkon shekara saboda zafi. Amma a wuraren da ake rikici, yara sun fi hadarin kamuwa da cutar.

Har yanzu riga-kafin kyanda a Najeriya ba ya kai wa ga yara da dama, sama da kashi 50 cikin 100 na yara ne ke samun rigakafin.

Hukumar Unicef ta bai wa ma'aikatan lafiya sama 1,000 horo a kan matakin gaggawa na farko a yankunan da ma'aikatan bayar da agaji ke iya zuwa a baya-bayan nan.

Hukumar ta kuma dauki wasu karin jami'an 60 aiki kuma ta tura likitoci shida domin karfafa aikin kiwon lafiya a yankunan.

Rikicin Arewa maso Gabashin Najeriya ya sa sama da mutum miliyan biyu da rabi sun bar muhallansu, yayin da fiye da 30,000 suka rasa rayukansu.