Makkah: An dakatar da binciken hatsarin ƙugiya

Alhazai a wurin da kugiyar ta rikito

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Alhazan Najeriya da dama sun rasa rayukansu a lokacin da hatsarin ya auku

Wata kotu a Saudiyya ta dakatar binciken da take yi a kan hatsarin rikitowar ƙugiya a masallacin Makkah da ya yi sandiyar mutuwar sama da alhazai 100.

Kotun ta ce bata da iko a hukamance da za ta zartar da hukunci a kan wasu mutum 14 da ake zargi da sakaci da lalata dukiyar jama'a da kuma yin watsi da ka'idojin lafiyar mutane.

Ba a ambato sunayen mutanen ba amma kuma rahotanni na cewa har da wani hamshakin mai kudi dan kasar.

Kugiyar ta rikito ne a lokacin da ake ruwan sama mai karfin gaske a shekarar 2015 dab da fara aikin hajjin shekarar.

Hatsarin ya faru ne a lokacin da ake aikin fadada masallacin wanda kamfanin Saudi Binladin ke yi.

A watan Satumbar shekarar 2015 ne dai sarki Salman na Saudiyya ya ce za a yi bincike dan gano musababbin faruwar hadarin.