Hauhawar farashi: 'Yan Nigeria na ɗanɗana kuɗarsu

  • Halima Umar Saleh
  • BBC Hausa, Abuja
Kasuwa a Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Farashin kayayyaki sun fara tashin gwauron zabi tun watan Fabrairun 2016

Tun a farko-farkon shekarar 2016 ne farashin kayayyaki ya fara tashin gwauron zabi a Najeriya, al'amarin da ya sa mutane suka shiga halin ha'u'la'i.

Farashin kayayyaki, musamman na abinci, ya ta tashi ba kama hannun yaro, har ta kai abinci na gagarar al'ummar kasar da dama.

A dabi'ar dan-Adam, a duk lokacin da aka shiga sabuwar shekara, ya kan dauka matsalolin da aka fuskanta a shekarar da ta gabata sun wuce ke nan sai a tarihi.

Amma a zahirin gaskiya ba haka batun yake ba, don kuwa an yi dakon matsalar hauhawar farashin, wadda aka fara cin karo da ita a watan Fabrairun 2016, zuwa sabuwar shekarar 2017, har ma masana tattalin arziki na ganin muninta ya fi na bara.

Hukumar kididdiga ta Najeriya ta fitar da rahoto a karshen watan Disamban da ya gabata, inda ta bayyana cewa farashin kayayyaki ya ci gaba da tashi a watanni 11 a jere.

A watan Disambar ne farashin kayayyaki ya tashi zuwa kashi 18.6 cikin 100 daga kashi 9.6 cikin 100 a farkon shekarar ta 2016.

'Hasashen 2017'

Hukumar kididdigar ta kuma yi hasashen cewa farashin zai ci gaba da karuwa zuwa kashi 18.71 a watan Janairu, da kashi 18.78 a watan Fabrairu, da kuma 18.84 a watan Maris din bana.

'Musabbabin hauhawar farashi'

Najeriya kasa ce da ke da dumbin arzikin man fetur da ma'adinai, sai dai ta fi samun kudin shigarta ne ta hanyar sayar da man fetur din ga kasashen duniya; hakan ya sa galibin kudin shigar da take samu daga waje ke fitowa daga cinikin man.

Tun a shekarar 2015 ne dai farashin danyen man fetur din ya fara faduwa a kasuwar duniya sakamakon yawan fitar da shi da ake yi, don haka yawan kudaden kasashen wajen da Najeriyar take samu ya ja baya sosai.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Najeriya ta dogara da samun kudin shigarta daga sayar da man fetur a kasashen duniya

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Sakamakon haka kuma mutane, musamman 'yan kasuwa, da ke shigo da kayayyaki suka fara fuskantar matsala wajen samun kudin musaya.

A duk kuwa lokacin da bukatar dala ta yi yawa to farashin dalar kan karu ne a hukumance da kuma a kasuwar bayan fage.

'Fargaba'

Ko a wannan makon ma an yi samu rahotanni daga bangarori daban-daban a kan yiwuwar dorewar wannan yanayi na tsadar rayuwa, da kuma kiraye-kiraye ga gwamnatin Najeriya kan cewa ta dauki matakan gaggawa don magance matsalar.

Misali, wani kamfanin zuba jari mai suna Afrinvest ya fitar da wani rahoto da ke cewa farashin kayayyaki zai ci gaba da hauhawa cikin hanzari a shekarar 2017 saboda yiwuwar kara farashin makamashi da kuma rage darajar kudi.

Ita ma kungiyar kwadago ta kasa, NLC, ta koka da yadda ake ci gaba da rufe masana'antu, al'amarin da ke jawo rashin aikin yi da tsadar kayan abinci da na bukata.

Shugaban reshen kungiyar na jihar Anambra ya ce, ''Albashin ma'aikata - wanda dama bai taka kara ya karya ba - a yanzu haka ba ya isa su sayi abinci balle sauran kayan bukatu.''

Shi ma jagoran jam'iyyar APC mai mulki kuma tsohon gwamnan Lagos, Asiwaju Bola Tinubu, ya yi irin wannan korafi, inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta daukar mataki.

Wani shahararren mawakin kasar ma, wato TuFace Idibia, ya yi kira ga 'yan Najeriya da su mara masa baya a zanga-zangar lumana da zai gudanar a watan Fabrairu don yin kira ga gwamnati ta san na yi a kan wannan batu.

Asalin hoton, Getty Images

'Halin ha'u'la'i'

Wannan al'amari ya jefa mutanen kasar cikin halin ka-ka-ni-ka-yi, har ta kai sun fara sukar gwamnatin Buhari da gazawa wajen cika alkawuran da ta yi na inganta abubuwa.

A wata muhawarar da Sashen Hausa na BBC ya shirya a shafinsa na Faceebook a kan ko an fara samun sauyi a halin da ake ciki na tsadar kayayyaki ko kuma da sauran rina a kaba, mutane daga sassan kasar daban-daban sun bayyana cewa, 'har yanzu ba ta sauya zane ba.'

Mafi yawan mutanen sun bayyana cewa 'a kulliyaumin farashin kaya kara hawa yake ba ya sauka.'

Ga kadan daga cikin sakwanni da mutane suka rubuta mana:

Shafi'u Abdu: "Gaskiya talaka yana cikin mawuyacin hali sakamakon wannan yanayi. Allah dai ya kawo mana mafita"

Haruna Boda Inkaibi: "A nan jiharmu ta jigawa ma haka matsalar take; babu wani abu mai sauki, batirin rediyo da muke saya N60 a da, yanzu N120 ne".

Bawa Abdullahi Maska: ''Farashin kayan masarufi ya kan tashi kusan kullum, idan ka sayi batir a kan naira 50 ba mamaki gobe ka ji an ce maka ya koma N60, kuma mun rasa inda laifin yake - a wurin 'yan kasuwa ne ko kuwa kamfanonin da ke sarrafa kayan masarufin ne?"

Mustapha Ibrahim Dan Malumfashi: "Rayuwarmu a yanzu ta yi wahalar gaske, saboda hauhawar farashin kaya, abin da ka saya yanzu a kasuwa, idan ka kai shi gida, ka dawo ka sake sayensa, to tabbas sai ka ji ya kara kudi maimakon ya rage. Gwamnati ba ta yin komai a kan hauhawar farashi saboda talakawa ne abin yake shafa."

Ahmed Elrufai Girei: "Gaskiya daya ce: ko ina a Nigeria komai ya yi tsada, yadda ake maganar nan gaba kadan komai zai yi sauki ba abin da ya sauya, haka abubuwa suke ta hauhawa don Allah ta ina talaka zai samu saukin rayuwa ne?"

Farashin wasu abubuwa a watan Janairun 2016 zuwa Janairun 2017

  • Buhun shinkafa babba N8000 - N19,500
  • Buhun Semovita N1,300 - N3000
  • Buhun fulawa N6,000 - N12,000
  • Kwanon dawa - N140 - N600
  • Kwanon wake N400 - N800
  • Kwanon sikari N400 - N900
  • Indomie N35 - N70
  • Tulun gas matsakaici (kilo 12.5) N2,500 - N5,300
  • Litar kananzir N100 - N500

'Ina mafita?'

Masana harkar tattalin arziki sun yi ta tsokaci a kan hanyoyin da za a bi a shawo kan wannan matsala da take sake gawurta.

Daga ciki akwai batun cewa dole babban bankin kasar, wato CBN, ya tsara wasu manufofi don tallafawa manoma da bangaren masana'antu da rance mai kudin ruwa kadan.

Kamar dai yadda Dokta Obadiah Mailafiya, wani tsohon mataimakin gwamnan babban bankin na Najeriya yake cewa, "Dole gwamnati ta tallafa wa manoma da isasshen taki da kayan aikin gona na zamani don magance matsalar hauhawar farashin abinci.''

Ya kuma ce akwai fargabar halin da za a shiga ciki nan da watanni biyu masu zuwa sai ya fi wanda ake ciki a yanzu muni.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba farashin kayan abinci ne kawai ya tashi ba har da na suturu ma

"Daga nan zuwa watan Maris da Afrilu kudin abinci zai rubanya fiye da yanzu, saboda manoma ba su da isassun kayan bukata don noma da kuma yawan tashe-tashen hankulan da ke sa musu fargabar zuwa gonar,'' in ji shi.

Da yake magana a kan CBN kuwa cewa ya yi:

  • Dole a dinga martaba manufofin babban bankin.
  • Dole kasuwar musayar kudi ta zama daya, saboda ana samun almundahana a wannan bangaren idan ya kasance akwai kasuwannin musayar kudi biyu a kasa.
  • A hanzarta kashe kudaden da aka ware don gudanar da ayyuka wadanda za su inganta rayuwar al'umma da kuma samar da ayyukan yi.

Haka kuma wasu masanan da dama na gargadin gwamnati cewa kada ta yi wani tunani na kara kudin harajin da take karba daga mutane.

Wannan ita ce matsalar hauhawar farashin kayayyaki mafi girma da aka samu a Najeriya cikin shekara 10 da ta gabata.

A yanzu dai a iya cewa 'yan Najeriya sun zuba ido don ganin ko gwamnati za ta dauki matakan shawo kan wannan matsala kafin shekarar nan ta yi nisa ko a'a.