Masana: Trump ya jefa duniya cikin hadari

Shugaba Donald Trump

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Masanan sun ce kalaman Trump sun kara jefa duniya cikin hadarin tashinta da wuri

Masana kimiyyar makamin kare-dangi sun ce lokacin tashin duniya ya kara matsowa sakamakon kalaman Shugaba Trump kan makaman kare dangi da batun sauyin yanayi.

Masanan wadanda suka matsar da hannun agogon da ke zaman alamar lokacin tashin duniyar a wurinsu, da dakika 30, sun ce a yanzu duniya ta kara shiga cikin hadari, sakamakon kalaman Shugaban na Amurka.

Agogon wanda aka kirkira a shekarar 1947, na zaman alamar fargabar da dan adam ke ciki ta tashin duniya.

Masana kimiyya da wasu kwararru kan harkokin duniya da suka hada da mutane 15 da suka ci lambar yabo ta Nobel su ne ke yanke shawarar matsar da hannun agogon ko kuma barinsa yadda yake.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

An kirkiri alamar ne (agogon) sakamakon fargabar tashin bam din kare-dangi ( atom) na farko

Yanzu dai an saita hannun agogon a karfe 12 na dre saura minti biyu da rabi, a matsayin lokacin da duniya za ta tashi.

Lokacin da aka kirkiri agogon a 1947, hannunsa na nuna karfe 12 na dare ne saura minti bakwai.

Kuma tun daga wannan lokacin, an sauya lokacin har sau 22, kama daga 12 dare saura minti biyu a 1953 zuwa 12 dare saura minti 17 a 1991.

Bayanan hoto,

Agogon da masana suka alamta da lokacin tashin duniya saboda abubuwan tashin hankali da ke faruwa

Lokaci na karshe da aka sake saita agogon zuwa wani lokacin shi ne a 2015 , sa'ilin da aka rage lokacin daga 12 saura minti biyar, zuwa sura minti uku, sakamakon batutuwa masu tayra da hankali da suka taso kamar su sauyin yanayi da bazuwr makaman kare-dangi.

Wannan shi ne lokacin da ya kasance mafi kusa a cikin sama da shekara 20.

A baya bayan nan, agogon yana kan karfe 12 na dare ne saura minti uku a 1984, lokacin da dangantaka tsakanin Amurka da tsohuwar Tarayyar Soviet (rasha) ta yi kamarin da ba ta taba yi ba.

Masanan sun ce wannan lokacin shi ne karon farko da suka matsar da hannun agogon gaba, saboda kalaman wani mutum daya.