''Yan jarida abokan hamayyar Trump ne'

Asalin hoton, Xinhua
A wani taron manema labarai, Trump ya soki tashar talabijin ta CNN da cewa tana watsa karerayi
Babban mai tsara wa Shugaba Donald Trump dabaru Steve Bannon ya bayyana kafafen watsa labarai a matsayin jam'iyyar hamayya ga sabon shugaban na Amurka.
Mista ya kara da cewa kamata ya yi jam'iyyar ta rufe bakinta ta kasa kunne kuma a yanzu.
A yayin wata hira da jaridar New York Times, Mista Bannon ya ce, ya kamata a ce kafafen watsa labarai sun ji kunya, kan yadda suka kasa tsinkayen nasarar Mista Trump.
Ya ce manyan 'yan jarida da dama sun nuna son-kai da goyon bayan Hillary Clinton.
Jaridar ta New York Times ta ce Mista Bannon, wanda ya yi kalaman ta waya, ya yi su ne a natse, kuma ba tare da wani kawaici ko alkunya.
Kafafen watsa labari dai sun ci gaba da samun rashin jituwa da fadar gwamnatin Amurkar, kana yawan taron mutanen da suka halarci rantsar da Shugaba Trump.
Sannan kuma da batun zargin da yake yi na cewa miliyoyin bakin haure sun kada kuri'ar kin zabensa.