Mayakan Al-Shabab sun kai wa sojojin Kenya hari a Somalia

Kenya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Ba wannan ne karon farko da al-Shabab ta kai hari a sansanonin rundunar sojin kasar Kenya a Somalia

Mayakan Al-Shabab sun kai hari a kan wani sansanin dakarun gwamnatin Kenya a kudancin Somaliya.

Kungiyar ta Al-Shabab mai nasaba da Al-Qaeda ta ce ta kashe sojoji fiye da 50 kuma ta kwace motocin soji da makamai.

Amma wani kakakin dakarun soji na Kenya ya ce an dakile harin wanda aka kai da asuba, ba a mamaye sansanin ba, kuma an kashe masu ta-da-kayar-baya da dama.

A shekara guda da ta wuce mayakan kungiyar ta Al-Shabab sun kaddamar da wani harin makamancin wannan a kan wani sansanin sojin Kenya a yakinda ke el-Ade.

Bayan harin na el-Ade kungiyar ta ce ta kashe sojoji fiye da 100, amma gwamnatin kasar Kenya ta ki bayyana yawan mutanen da suka rasa rayukansu.

Kenya ta bayar da sojoji fiye 3,600 ga rundunar Tarayyar Afirka da ke taimaka wa gwamnatin Somaliya mai samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya yakar Al-Shabab.