Majalisar dokokin Rasha ta amince da kudurin dokar sassauta cin zarafin mata

Rasha

Asalin hoton, PA

Bayanan hoto,

Mutane ruba'i ke mutuwa sakamakon cin zarafin mata a cikin gida

Majalisar wakilan ta ce idan kudurin ya zama doka duk wanda aka kama da laifin cin zarafin mace a karon farko, kuma bai ji mata rauni sosai ba, za a tsare shi ne na kwana 15 a caji ofis maimakon shekara biyu a gidan kurkuku.

A halin yanzu dai ana bukatar majalisar dattawa ta amince da dokar da kuma sa hannun shugaba Vladimir Putin.

Masu lura da a'lamura sun ce dokar da aka yi wa lakabi da suna "Dokar mari " na nufin ''an ba da damar cin zarafin mata a gida ke nan''.

Wato sakon da dokar ke aikewa ita ce: 'Kada mu hukunta mutumin da ke dukan iyalinsa a gida saboda suna da ikon yin hakan''.

Majalisar wakilai 380 suka amince da dokar, yayin da 'yan majalisar uku ne kawai basu amince da ita ba.

Bincikin da hukumar cikin gida ta Rasha ta gudanar na nuna cewa mata 9,800 ne suka mutu sakamakon cin zarafi a shekarar 2015 kuma rabinsu sun fuskanci cin zarafin ne a cikin gida.

Abin da ke nuni da cewa ana kashe mata 600 duk wata a gida.

Wata mai kare hakkin mata, Alena Popova da ke kira a yi dokar da zata kunshi komai da kamai game da yaki da cin zaramin mata ta samu sa hannun kusan mutane 239,000.